Martanin Jama’a Kan Bidiyon da Aka Ba Dama Ta Kwashi Komai Take So Cikin Dakiku 30 a Kantin Siyayya

Martanin Jama’a Kan Bidiyon da Aka Ba Dama Ta Kwashi Komai Take So Cikin Dakiku 30 a Kantin Siyayya

  • Wata budurwa ‘yar Najeriya da aka ba ta damar daukar duk abin da ta ga dama a kantin siyayya cikin dakiku 30 ta rude
  • Budurwar ta rasa abin da za ta dauka, sai kawai ta fara tattara fakitin ruwa da gwangwanayen abincin kare da sauransu
  • Da yawan ‘yan Najeriya da suka ga bidiyon sun yi mamaki, wasu suka ce ta yi wasa da dama, ina ma su aka ba damar

Wani dan Najeriya, @ositapopcorn ya hada wani bidiyo mai daukar hankali na yadda ya ba wata budurwa damar siyayya kyauta a kantin siyayya.

Ya fada wa budurwar cewa, dukkan abin da hannunta ya kai dauka a cikin dakiku 30 nata ne, zai biya kudin, lamarin da ya faranta mata rai.

Bayan kirge, da umartarta da fara dauka, budurwar ta ruga, inda ta fara daukar kayayyakin sha na ruwa. A lokacin, ta dauki fakitin ruwa ta tafi dashi.

Matashi ya ruda budurwa a kantin siyayya, ya ce ta dauki komai cikin dakiku 30
Bidiyon matashin da ya sanya budurwa gudu a kantin siyayya | Hoto: @ositapopcorn
Asali: TikTok

Cikin kuskure, ta dauki abincin kare duk da kuwa bata da karen a gida. Mutane da yawa sun ce ta kwafsa, dama su suka samu dama irin wannan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Martanin jama’a

Legit.ng ta tattaro muku kadan daga abin da mutane ke cewa kan wannan bidiyo mai daukar hankali.

@Ilham:

"Ina nan ina ta ihun ga can shinkafa.”

@Zugwai:

"Kalli shinkafa, don Allah nan ina ne, zan sanya hijabi na saka saboda na samu abin da zan ci.”

@Queenniffy29:

"Har na gama shirin yadda zan dauki buhunnan shinkafa hudu na tafi.”

@Ennie Olar:

"Ta dan rude ne saboda bata yi tsammanin hakan ba. Ba kama ta ba, ni dama ina son warwaso.”

@i_am_starbee:

"Idan ka fada hannu ba, kalli buhun shinkafa a gefe fa.”

@Chioma Lawrence30:

"Kina kallon buhun shinkafa kina daukar kwalin biskit. Najeriya ce ta ja mana.”

@memes and funny videos:

"Don Allah meye yasa bata dauki maltina da shinkafa ba.”

@EuniceMentus:

"Duk ranar da naje kanti wani ya gwada wannan dani ranar Allah ne kadai zai cece shi don na rantse ko mota suke siyarwa a wurin sai na dauka.”

@Ajumaji1:

"Idan nine inda buhunnan shinkafa suke nan zan tafi na dauki adadin da ya sauwaka cikin dakiku 30.”

@Testimony:

"Don Allah meye zan yi da abin sha?”

Kowa da kiwon da ya karbe shi, wani kuma zaki yake kiwo na tsawon shekaru 11 kenan yana abu daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel