Rayuwa ba Tabbas: Yadda Sanata Bello Mandiya Ya Rasu bayan Ya Shiga Banɗaki a Gidansa

Rayuwa ba Tabbas: Yadda Sanata Bello Mandiya Ya Rasu bayan Ya Shiga Banɗaki a Gidansa

  • Sanata Abdul Ningi ya bayyana cewa yadda tsohon sanstan Katsina ta Kudu, Bello Mandiya ya rasu a banɗaki a gidansa da ke Abuja
  • Rahotanni sun nuna cewa ab gano gawar Mandiya bayan kimanin sa'o'i 72 da rasuwarsa bayan wani wari ya fara fita daga gidan
  • Sanata Bello Mandiya ya wakilci mazaɓar Katsina ta Kudu a Majalisar Dattawa daga 2019 zuwa 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sanata Abdul Ningi ya bayyana yadda abokin aikinsa, Bello Mandiya, ya rasu bayan ya zame a banɗaki ya bugi kansa, inda aka gano gawarsa bayan kimanin sa'o'i 72 a gidansa da ke Abuja.

Ningi, wanda ke wakiltar mazaɓar Bauchi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, ya ce maƙwabta ne suka gano gawar Mandiya bayan wani wari ya fara fita daga gidansa.

Kara karanta wannan

Kwana ya ƙare: Mawakin addini a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Bello.
Tsohon sanatan Katsina ta Kudu, Marigayi Bello Mandiya Hoto: Ibrahima Kaula Mohammed
Source: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa yayin da yake magana yayin zaman majalisar dattawa, Ningi ya ce yana Saudiyya lokacin da ɗansa ya kira shi ta waya ya sanar da shi rasuwar Mandiya.

Ya ce ɗansa na cikin mutanen da suka gano gawar tsohon ɗan majalisar a ranar Litinin, 7 ga Satumba, 2026.

Yadda Sanata Bello Mandiya ya rasu

Da yake bayyana abubuwan da suka faru kafin gano gawar, Ningi ya ce wani abokin aikinsu ya ga Mandiya karo na ƙarshe da misalin ƙarfe 11:00 na safe ranar Juma'a, 4 ga Satumba, kafin tsohon sanatan ya koma gidansa, inda yake zama shi kaɗai.

A cewarsa, Sanata Mandiya yana shirin zuwa sallar Juma'a ne lokacin da aka ce ya zame bayan ya yi wanka, ya bugi kansa.

Ningi ya ce:

“Ya fito da hularsa da wayoyinsa, ya ajiye su a kan gado, sannan ya shiga banɗaki domin yin wanka.
“Bayan ya gama wanka, lokacin da yake fitowa daga banɗakin, sai ya zame ya bugi kansa a cikin banɗakin.”

Kara karanta wannan

Ana shirin zaben 2027, shugaban INEC ya mika dukan lamuransa ga Ubangiji

Yadda aka gano gawar Sanata Mandiya

Abdul Ningi ya ce babu wanda ya fahimci abin da ya faru har sai da warin da ke fitowa daga gidan Mandiya ya fara bazuwa zuwa gidajen maƙwabta.

Ya shaida wa Majalisar Dattawa cewa: “Tsawon sa'o'i 72, Mai Girma Shugaban Majalisa, babu wanda ya san inda Bello Mandiya yake.”

Ya ce babban limamin masallacin Apo ma ya fara nuna damuwa bayan ya lura cewa Sanata Mandiya, wanda ya saba yin salloli biyar na kowane rana tare da sauran Musulmi, bai halarci sallah ba har tsawon kwanaki uku a jere.

Ningi.
Sanata Abdul Ningi, wanda ke wakiltar mazaɓar Bauchi ta Tsakiya a Majalisar Dattawa Hoto: Abdul Ningi
Source: Facebook

Damuwa da limamin ya nuna da kuma warin da ya fara fita daga gidan ne suka sa mazauna yankin suka yanke shawarar bincika abin da ke faruwa a gidan.

Ningi ya ce daga ƙarshe mutanen da suka je gidan sun fasa ƙofar, inda suka tarar da gawar Mandiya a banɗaki.

Ya ce: “Ga Bello Mandiya a kwance a cikin banɗaki, ba rai. Sa'o'i 72 kenan, kuma wannan babban abin takaici ne.”

Kara karanta wannan

Fasto ya gano Atiku na da sa'a a 2027, ya ce Tinubu zai iya faduwa warwas

Ningi ya yi jimamin rasuwar Mandiya

Da yake bayyana alhininsa kan yadda abokin aikinsa ya rasu, Ningi ya ce lamarin ya nuna yadda rayuwa take da rashin tabbas, domin babu wanda zai iya sanin lokacin da mutuwa za ta zo masa.

Ya kuma mika ta'aziyyarsa ga iyalan Mandiya, al'ummar Jihar Katsina da kuma mutanen da ya wakilta a Majalisar Dattawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262