“Za Ka Sha Garin Kwaki”: Matashiya Ta Koka Bayan Danta Ya Zubar Da Madarar N16k a Bidiyo

“Za Ka Sha Garin Kwaki”: Matashiya Ta Koka Bayan Danta Ya Zubar Da Madarar N16k a Bidiyo

  • Wata yar Najeriya ta gano karamin danta yana barnatar da madarar gwangwani da ta siya N16k kuma hakan ya bata mata rai
  • Uwar da ranta ya baci ta koka a shoshiyal midiya, tana mai cewa yaron ya barnatar da madarar a lokacin da ake wahalar kudi
  • Jama'a sun yi martani kan bidiyon yayin da wasu suka zarge ta da neman suna wasu kuma sun soke ta kan rashin adana shi inda hannun yaron ba zai kai ba

Wata mata yar Najeriya ta garzaya soshiyal midiya domin yin korafi cewa danta ya barnatar da gwangwanin madarar N16k.

Ta wallafa wani bidiyo a TikTok da ke nuna yaron wanda babu abun da ya dame shi zaune dumu-dumu cikin madara da gwangwanin a gefensa.

Uwa da danta da ya zubar da madara gwangwani daya
“Za Ka Sha Garin Kwaki”: Matashiya Ta Koka Bayan Danta Ya Zubar Da Madaran N16k a Bidiyo Hoto: @realrerri
Asali: TikTok

Yaron ya ci gaba da wasa da madarar yayin da take kokari da nuna rashin jin dadinta kan abun da ya aikata.

Kara karanta wannan

“Ka Duba Darajarmu Idan Ta Yi Laifi”: Bidiyon Uban Amarya Yana Yi Wa Surukinsa Nasiha Mai Tsuma Zuciya a Ranar Aurensu

Ta koka cewa yaron ya barnatar da madarar a daidai lokacin da samun tsabar kudi ya zama babban matsala kuma cewa dole ya fara shan garin kwaki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bidiyon na TikTok ya haifar da martani daban-daban. Wasu sun caccake ta kan kin ajiye tsadadden madarar a inda hannun yaron ba zai kai ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@OLUWASEUN ta ce:

"Wannan abun na da mafita, yaron bai barbaza shi ba, ki tattara, kina masa ihu me ya dame shi."

@beautytalks25 ta ce:

"Kin dauki gwangwani ba komai kin basa sannan kika zuba madara mai araha a kasa kina ihun liyan. Hajiya je ki huta kina da kudi.

@AmakaEmmanuel ta ce:

"Sannu da aiki.
"Tsaya nan kina ihun Leyam, zai tattara maki, mama lili."

@neche ta ce:

"Me zai sa ki ajiye madarar 16k inda hannunsa zai kai, madarar 1500 kawai, ina boye hi inda dana ba zai gani ba."

Kara karanta wannan

Dattijuwa Ta Samu Cikin Fari Tana Da Shekaru 54, Allah Ya Azurta Ta Da Yan Uku a Bidiyo

@edoziunoifeoma ta ce:

"Allah ya kiyaye...saraki ba za ka sha Garin kwaki ba...Allah zai ci gaba da ho re ma iyayenka."

Matashi ya samu tallafi, zai tafi Turai karatu

A wani labari na daban, mun ji cewa Allah ya tarbawa garin wani yaro da yake yawo a titi nono inda wasu suka taimaka masa da makudan kudade, an kuma yi masa hanyar tafiya Turai karatu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel