"Ba Musulmai ba ne," Shugaban Majalisa Ya Gano Wadanda Suka Hana Zaman Lafiya a Najeriya
- Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce sama da 70% na mutanen da ke haddasa tabarbarewar tsaro a Najeriya ba ’yan ƙasar ba ne
- Akpabio ya bayyana hakan ne yayin da yake kare matsayinsa kan kudirin dokar da ke neman cire laifin yunƙurin kashe kai daga cikin laifuffukan doka
- Ya jaddada cewa addinin Musulunci da Kiristanci ba sa koyar da ta’addanci, yana mai cewa bai kamata a danganta yan ta'adda da wani addini ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce sama da kashi 70 na yan ta'addan da suka hana zaman lafiya a Najeriya ba ’yan ƙasar ba ne.
Sanata Akpabio ya bayyana haka ne yayin da yake mayar da martani kan sukar da ake yi masa game da matsayinsa kan kudirin dokar cire laifin yunkurin kunar bakin wake daga kundin laifuffuka.

Source: Facebook
Premium Times ta ce Akpabio ya bayyana hakan ne yayin zaman Majalisar Dattawa na ranar Alhamis, bayan wasu mutane sun soki matsayinsa kan kudirin dokar da aka karanta a karo na biyu.
Kudirin dokar na neman cire yunƙurin kunar bakin wake daga cikin laifuffukan da doka ta tanada, tare da samar da tsarin doka da zai taimaka wajen dakile hakan, jinya da tallafa wa waɗanda suka tsira daga yunƙurin kashe kansu.
Dalilin sukar Sanata Akpabio
Tun bayan da kudirin ya tsallake karatu na biyu, wasu yan Najeriya suka zargi Akpabio da nuna son kai ga Musulunci, musamman saboda nacewarsa cewa ya kamata a daure mutanen da aka samu da laifin yunƙurin kashe kansu.
Da yake mayar da martani, Akpabio ya musanta nuna wariya ga wani addini. Ya bayyana sukar da ke masa a matsayin siyasa.
Ya ce babu daya daga cikin addinan Musulunci ko Kiristanci da ke koyar da ta’addanci, yana mai jaddada cewa bai kamata a danganta masu aikata irin waɗannan laifuka da wani addini ba.
“Ya kamata ku sani cewa ’yan ta’adda ba Musulmi ba ne. ’Yan ta’adda ba Kiristoci ba ne. ’Yan ta’adda mutane ne da suka yi imani da ɗaukar rayukansu da kuma rayukan wasu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa wasu jihohin Najeriya ba sa fuskantar matsalar harin kunar bakin wake, amma akwai mutanen da ke aikata irin waɗannan hare-hare saboda shan miyagun ƙwayoyi ko neman kuɗi.
“Waɗannan mutanen ba sa cikin wani addini,” in ji Akpabio.

Source: Facebook
Akpabio ya fadi hukuncin Musulunci
Shugaban Majalisar Dattawan ya ce Musulunci ya haramta kashe kai da kuma kashe wasu mutane. Ya ƙara da cewa Alƙur’ani ya yi gargaɗi game da kashe kai.
“Addinin Musulunci kamar yadda na sani ya haramta kashe kai. Ya haramta kisa. Addinin Musulunci kamar yadda na sani ba ya yarda mutum ya kashe kansa.
"Idan ka duba Alƙur’ani, za ka ga cewa ya haramta kashe kai. Haka kuma ya bayyana cewa idan mutum ya kashe kansa, ba zai shiga Aljanna ba,” in ji shi.
Akpabio ya gargadi gwamnonin APC
Kun ji cewa shugaban Majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya gargadi gwamnonin jam’iyyar APC da kada su yi watsi da al’ummarsu saboda neman wasu mukaman siyasa da ba za su samu ba.
Akpabio ya bukaci gwamnonin da su mayar da hankali wajen kammala wa’adin mulkinsu na shekaru takwas, wanda kundin tsarin mulki ya ba su damar yi.
Asali: Legit.ng

