EFCC Ta Cafke Dan Babban Shehin Darika a Najeriya kan Badakala

EFCC Ta Cafke Dan Babban Shehin Darika a Najeriya kan Badakala

  • Hukumar EFCC shiyyar Jihar Kano ta gurfanar da Abdulmajid Halifa Nazifi Al-Karmawi a gaban kotu kan zargin karkatar da naira miliyan 34.8
  • Matakin da hukumar ta ɗauka ya biyo bayan zarginsa da amfani da kuɗin da aka tura masa domin sayen kayan abinci zuwa buƙatun kansa
  • An gurfanar da wanda ake zargin ne a ranar Laraba, 14 ga watan Okutoba, 2026 a gaban Mai Shari'a Musa Karaye na Kotun Ƙoli ta Jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Hukumar EFCC reshen Jihar Kano ta gurfanar da Abdulmajid Halifa Nazifi Al-Karmawi a gaban Mai Shari'a Musa Karaye na Kotun Ƙoli ta Jihar Kano a kan zargi guda ɗaya na karkatar da kuɗi har N34,875,000.00.

Wanda ake zargin ya bayyana a gaban kotun ne a ranar Laraba, 14 ga watan Okutoba, 2026.

Kara karanta wannan

Samaila Kaigama ya fara fuskantar hukunci kan zargin taimaka wa 'yan ta'adda a Najeriya

Abdulmajid Halifa Nazifi Al-Karmawi
Abdulmajid Halifa Nazifi da EFCC ke zargi da badakala. Hoto: EFCC
Source: Facebook

EFCC ta wallafa a Facebook cewa an tuhumi wanda ake zargin da karkatar da kuɗin da aka tura masa ta asusun Muazu Abdullahi da ke bankin First Bank domin sayen taliyar IRS daga kamfanin BUA.

Ana zargin cewa ya yi amfani da su wajen biyan buƙatun kansa sabanin yarjejeniyar da aka yi.

Tuhumar da ake masa

EFCC ta ce abin da ya faru tsakanin Satumba da Oktoban 2024 a Kano ya sabawa sashe na 308 na dokar Jihar Kano, wanda kuma ke fuskantar hukunci a ƙarƙashin sashe na 309 na wannan doka.

Bayan an karanta masa tuhumar, Abdulmajid Halifa Nazifi ya bayyana cewa ba shi da laifi, wato bai amsa laifinsa ba.

EFCC ta bayyana cewa:

"Sakamakon rashin amsa laifinsa, lauyan masu shigar da ƙara, Mustapha Maiwada, ya buƙaci kotun da ta sa ranar saauraren shari’ar sannan ta ba da umarnin tsare da wanda ake zargin a gidan yari."

Kara karanta wannan

Ana shirin zaben 2027, shugaban INEC ya mika dukan lamuransa ga Ubangiji

An mika Abdulmajid kurkuku

Mai Shari'a Karaye ya ba da umarnin tura wanda ake zargin zuwa gidan yari har zuwa ranar 2 ga watan Nuwamba, 2026 wanda aka ɗaga sauraron shari’ar.

An bayyana cewa Halifa da yake fuskantar wannan shari'a ɗa ne ga sanannen malamin ɗariƙa a Jihar Kano, Sheikh Nazifi Al-Karmawi.

A cewar lauyan masu shigar da ƙara, ana sa ran kotu za ta gudanar da cikakken sauran shari'ar domin tabbatar da adalci ga wanda aka cuta.

EFCC ta ce:

"Kotun ta amince da bukatar lauyan masu ba da kariya na ajiye wanda ake zargi a gidan gyaran halin kafin ranar sauran shari'ar."
Taswirar jihar Kano
Taswirar jihar Kano. Hoto: Legit
Source: Original

EFCC za ta binciki Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa Hukumar EFCC ta tabbatar da sake buɗe bincike a kan zarge-zargen da ake yi wa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar.

Kara karanta wannan

'An yi awa 9,' Yadda aka kai har dare ana shari'ar El Rufa'i a Kaduna

A cewar wata takardar yarda da aka ambata a rahotannin ranar Laraba, hukumar ta fara bincike ne kan batutuwan da tsohon ɗan majalisar wakilai, Ehiozuwa Johnson Agbonayinma ya gabatar.

Sabon binciken na zuwa ne yayin da Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC, yake shirin ƙalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng