‘Ba Zan Iya Auren Mai Albashin N70k Ba’: Kalaman Budurwa Sun Tada Kura a Kafar Sada Zumunta

‘Ba Zan Iya Auren Mai Albashin N70k Ba’: Kalaman Budurwa Sun Tada Kura a Kafar Sada Zumunta

  • Wata budurwa ‘yar Najeriya ta ce ba za ta iya auren mutumin da albashinsa N70,000 bane, ta jawo cecekuce
  • Budurwar ta nuna alamar turbune fuska tare da cewa ai kudin sun yi kadan wajen kula da ita, ta bayyana dalilinta
  • ‘Yan Najeryan da suka yi martani a bidiyon sun ce ta yi ganganci, domin ba kowa ne cikin ma’aurata ke samun N70k ba

Wata kyakkyawar budurwa ‘yar Najeriya ta bayyana irin ‘yan albashin da ba za ta iya aura ba a wani bidiyon da @kikiotolu ya yada.

Budurwar ta ce, ba za ta iya auren mutumin da ke samun N70,000 ba a wata. Ta kara da cewa, kudin sun yi kadan wajen kula da alakarsu.

Ga batun aure kuwa, ta ce kudin sun yi kadan, domin ta san aukin kudin saboda ita ma N70,000 take samu duk wata.

Kara karanta wannan

Assha: Bidiyon yadda matashi ya ba budurwa damar daukar duk da abin take so a kanti cikin dakiku 30

Ba zan auri mai albashin N70k ba, inji wata budurwa
Budurwar da tace ba za ta aurei mai albashin N70k ba | Hoto: @kikiotolu
Asali: TikTok

Amsan da ta bayar bayan tambayarta ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta, mutane da yawa sun yi martani mai daukar hankali.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton, bidiyon ya samu martani sama da 2000 da kuma dangwalen nuna sha’awa sama da 18,000.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Legit.ng ta tattaro muku kadan daga abin da mutane ke cewa:

@user3114430493435:

"Ko da mijina N45k yake samu amma muna raye da albarkar ubangiji.”

@gabrielujah5:

"Ina samun 40k a lokacin da na yi aure amma yanzu ina samun sama da 350k.”

@Ebirim Uche Prince-bernard:

"Idan ina samun 70k a wata ba zan yi aure ba.”

@TELEGRAM:

"Ni mutum ne da ba zan auri yarinyar da ke samun N70k ba.”

@Edweirdo:

"Meye zai sa mutum ya so aure da albashin 70k a wannan kasar? Akwai damuwa!!!”

Kara karanta wannan

Dattijuwa Ta Samu Cikin Fari Tana Da Shekaru 54, Allah Ya Azurta Ta Da Yan Uku a Bidiyo

@user samueljames:

"Lallai kinga miji araha ne.”

@user4112698662145:

"Wannan na nufin mu da muke samun 10k a wata aure ba namu bane kenan. Allah kai mana rahama.”

@Michael4god:

"70k+70k ya zama 140k amma a haka kika ce ya yi kadan amfani dake zan yi na yi tsafi kawai.”

An ruda budurwa a kantin siyayya

A wani labarin, matashi ya ruda budurwa a kantin siyayya yayin da ya ba ta damar daukar duk abin da take so cikin dakiku 30.

Bidiyon ya nuna lokacin da budurwar ke tattara kayayyaki, ta dauki abincin kare da kuma fakitin ruwa.

Jama’ar kafar sada zumunta sun yi martani, sun ce bata san ma abin da take bukata ba, ga kayayyaki da yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel