“Ka Yafe Mata”: Uban Amarya Ya Shawarci Mijin Diyarsa a Ranar Aurensu a Bidiyo

“Ka Yafe Mata”: Uban Amarya Ya Shawarci Mijin Diyarsa a Ranar Aurensu a Bidiyo

  • Wani suruki ya shawarci mijin diyarsa kan abubuwan da ya kamata ya yi domin samun rayuwar aure mai dadi
  • Mutumin ya fada ma angon cewa ya zamo mai tsananin hakuri a auren sannan ya zama mai yafiya ga matar tasa
  • Uban amaryar ya ce a duk lokacin da matar ta yi masa laifi, sai ya duba mutuncin iyayenta da yake gani

Wani uba a bidiyon aure da shafin @jidegoldalagasat ya wallafa ya zaunar da diyarsa da mijinta domin yi wa angon nasiha a bainar jama'a.

A bidiyon, ya fada ma mijin da ya zamo mai tunani a auren a duk lokacin da matar ta yi ba daidai ba. Uban ya kara da cewar babu auren da bai da matsaloli.

Amarya, mahaifinta da kuma angonta
“Ka Yafe Mata”: Uban Amarya Ya Shawarci Mijin Diyarsa a Ranar Aurensu a Bidiyo Hoto: @jidegoldalagasat
Asali: TikTok

Suruki na yi wa angon diyarsa nasiha

Kara karanta wannan

Duk Wayon Amarya: Uba Ya Shayar Da Dansa Bayan Ya Sanya Hoton Fuskar Mahaifiyar Yaron a Nasa, Bidiyon Ya Yadu

Uban amaryar ya fada ma angon cewa matashiyar ta fi shi karancin shekaru kuma ya kamata ya dunga duba tsawon shekarun da suka kwashe suna soyayya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake karin maganar Yarbawa, mutumin ya ce:

"Ba za mu iya tafiya ba tare da kanmu ya motsa ba."

Ya bukaci angon kan ya kulan masa da diyarsa koda kuwa ta yi masa laifi. Masu TikTok da dama sun so irin shawarar da surukin ya baiwa mijin diyar tasa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@jeje gently ta ce:

"Amaryar na tsoro, kada baba ya kauce hanya. An Gode Allah Baba Bai sha ya yi mankas ba."

@s ta ce:

"Wannan shine uba nagari......, Allah ya albarkaceka dadi."

@Rawdat ta ce:

"Shawara mai kyau. Allah ya albarkaci iyayenmu Allah ya sa su ci moriyar haihuwarsu inshallah."

Kara karanta wannan

Yadda Budurwa Yar Najeriya Ta Roki Saurayinta Bayan Ta Kama Shi Yana Cin Amanarta, Hirarsu Ta Bayyana

@Tobiloba ta ce:

"Na kaunaci wannan mutumin da dukkan zuciyata ina rokon Allah ya bani irin wannan surukin."

@KingOfSuccess ya ce:

"Wannan irin uba, Allah ya albarkaceka yallabai. Shawara mai kyau daga uba nagari....Allah ya albarkaci angon."

@lovethayomipo ya ce:

"Ma shaa Allah! Ina tsananin kaunar mutumin nan, yana kaunar diyarsa, hakan ya nuna. Mahaifina kenan, mai son zaman lafiya, kwakwalwa mai albarka."

Bayan shekaru 17 da aure, ma'aurata sun gano su yan uwa ne

A wani labari na daban, wasu ma'aurata sun gano ashe dai suna da alaka ta jini a tsakaninsu bayan sun haifi yara uku tare a cikin shekaru 17.

Asali: Legit.ng

Online view pixel