“Dan Allah Kada Ka Barni”: Kyakkyawar Budurwa Ta Roki Saurayinta Bayan Ta Kama Shi Yana Cin Amarta

“Dan Allah Kada Ka Barni”: Kyakkyawar Budurwa Ta Roki Saurayinta Bayan Ta Kama Shi Yana Cin Amarta

  • Wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya ta bayyana yadda ta roki tsohon saurayinta kan kada ya rabu da ita bayan ta kama shi yana cin amanarta
  • Ta aika masa sako tana mai ba shi hakuri ba tare da wani dalili ba kuma cewa yana iya fita da duk yarinyar da yake so
  • Hoton hirarsu da tsohon saurayin nata ya haifar da zafafan martani a dandalin soshiyal midiya

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta wallafa yadda ta roki tsohon saurayinta bayan ta gano cewa yana cin amanarta.

Matashiyar ta saki hirar da suka yi da shi ta WhatsApp yayin da ta magantu a TikTok game da yadda ta kusa kashe kanta.

Kyakkyawar budurwa da hirarsu da saurayinta
“Dan Allah Kada Ka Barni”: Kyakkyawar Budurwa Ta Roki Saurayinta Bayan Ta Kama Shi Yana Cin Amarta Hoto: @prettymarvel08
Asali: TikTok

Ta yi kokarin farfado da soyayyarsu bayan ta gano cewa ya fara juya mata baya amma ya ki sauraronta.

Budurwar ta yi amfani da dadadan kalamai yayin da take rokonsa a kan kada ya rabu da ita, cewa bata ma yi fushi ba duk da ta kama shi yana cin amanarta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Saboda yadda idonta ya rufe da sonsa, har cewa ta yi yana iya fita da duk yarinyar da yake so don kawai kada ya rabu da ita.

Matashin ya shawarce ta da ta ci gaba da rayuwarta ba tare da shi ba.

Kalli wallafarta a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Gideon Nabel ta ce:

"Kana iya fita da kowace yarinya da kake so amma dan Allah kada ka rabu da ni.
"Allah na roke ka, kada na zauce ya kai wannan matakin."

@Lucky Princewill ya ce:

"Kada ka kuskara ka roki wani ya so ka.
"Kawai za ka basu kafar rainaka ne sosai.

"Idan suna son tafiya kawai ka barsu.
"Akwai abun da ya fi maka kasancewarsu a rayuwa."

@Jennie ta ce:

"Duk son da nake yi wa mutum ba zan taba bari wata mace ta kasance a tsakani ba."

@BigMummyJ ta ce:

"Kyakkyawa kamar ki kina rokon soyayya, dan Allah rabu da gayen nan bai cancanci samunki ba."

Matashiya mai masoya biyu ta magantu kan rayuwar aurensu

A wani labarin kuma, wata matashiya wacce ke da mazajen aure har biyu ta bayyana cewa kowannensu na da rawar ganin da yake takawa a rayuwarta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel