Bola Tinubu
Bola Ahmed Tinubu ya umurci Ahmad Lawan, shugaban majalisar dattawa ta 9 da Femi Gbajabiamila, kakakin majalisa ta 9 su warware rikicin shugabancin majalisa.
Ganin yadda ya yi mulki a Legas, Adaku Ogbu-Aguocha ta ce sabon shugaban kasa zai cigaba da nasarori a gwamnatinsa, ta na fatan Tinubu zai hada-kan al’umma.
Sanata Oluremi Tinubu ta fara shiga ofishinta na matar shugaban ƙasa ranar Litinin 5 ga watan Yuni, 2023 bayan rantsar da mijinta a matsayin shugaban Najeriya.
Shugaban kungiyar Gwamnonin APC, Hope Uzodinma ya ce Tajuddeen Abbas/Ben Kalu sun fi cancanta da rike majalisa. Uzodinma ya hadu me da masu goyon bayan Abbas.
Za a ji labari Festus Keyamo SAN bai yi nasara a karar da ya shigar a kotun tarayya a kan Alhaji Atiku Abubakar ba. Tsohon Ministan zai lalo kudi ya biya Atiku.
Ibrahim Gambari, shugaban ma’aikatan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mika mulki ga magajinsa, Femi Gbajabiamila a ranar Litinin, 5 ga watan Yuni.
Sanatoci sun ce ma’aikatun gwamnati sun karbi bashi, amma har yau ba su biya ba. Ana zargin Akanta Janar da sakacin wajen karbo wadannan kudi tun shekarar 2007.
Femi Gbajabiamila wanda zai zama shugaban ma’aikatan fadar gwamnati ya ce an cin ma wasu matsaya a sakamakon zaman da suka yi a Aso Rock kan batun yajin-aiki.
Kungiyar 'Yan Kasuwa, TUC ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kara mafi karancin albashi zuwa N200,000 don rage radadin cire tallafin mai da ya yi a kasar
Bola Tinubu
Samu kari