Muslim-Muslim: Kotu Ta Yi Fatali da Karar da Aka Shigar da Tinubu da Shettima

Muslim-Muslim: Kotu Ta Yi Fatali da Karar da Aka Shigar da Tinubu da Shettima

  • Babbar Kotun tarayya ta yi watsi da karar da aka nemi soke takarar Bola Tinubu kan hada Musulmi da Musulmi
  • Lauya mazaunin Abuja, Osigwe Momoh ne ya shigar da karar inda ya nemi kotun ta dakatar INEC daga amincewa APC ta shiga zabe
  • Alkalin Kotun mai shari'a Mohammed, ya ce lauyan ba shi da hurumin kalubalantar takarar Tinubu

Abuja - Babbar Kotun tarayya mai zama a birnin tarayya Abuja ta yi fatali da ƙarar da aka shigar da Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa a APC.

Alkalin Kotun mai shari'a Ahmed Ramat Mohammed shi ne ya yi fatali da karar, wacce aka bukaci soke takarar Tinubu kan haɗa tikitin Musulmi da Musulmi a zaben 2023.

Yan takarar APC
Muslim-Muslim: Kotu Ta Yi Fatali da Karar da Aka Shigar da Tinubu da Shettima Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Channels tv ta rahoto cewa wani Lauya a Abuja, Mista Osigwe Momoh, ne ya shigar da karar kuma Alkalin ya fatattaki bukatarsa ne saboda lauyan ba shi da ikon sa baki a batun.

Kara karanta wannan

Akwai Ƙura: “Ba a Gina Makarantar da Tinubu Yake Ikirarin Ya Yi Karatun Boko ba”

Mai shari'a Mohammed ya bayyana cewa kasancewar lauyan ba mamba bane a APC kuma ba da shi aka bi matakan samar da Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima ba, ba shi da hurumun kalubalantar takararsu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Meyasa lauyan ya shigar da ƙara Kotu?

A ƙarar da ya shigar, lauyan ya roki Kotu ta haramtawa APC da Tinubu shiga zaben shugaban ƙasa mai zuwa bisa Hujjar haɗa takara Musulmi da Musulmi.

A cewar Lauyan matakin ya saba wa kundin tsarin Mulkin Najeriya kuma ya yi karan tsaye ga sashi na 14, 15 Da 224 a kwansutushin ɗin Najeriya 1999, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Haka zalika mai shigar da karar ya nemi Kotu ta dakatar da hukumar zabe INEC daga sanya sunan APC da ɗan takararta na shugaban kasa dangane da zaben 2023.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: NRM Ta Maka Peter Obi A Kotu Kan Zargin Mallakar Takardun Izinin Zama Dan Kasashe Biyu

Sai dai a hukuncin da Kotu ta yanke, mai shari'a Mohammed, ya ƙi yarda da musun Lauyan game da damar da doka ta bayar na kai kara kan batun kana ya yi watsi da ita baki ɗaya.

A wani labarin kuma Dan takarar shugaban kasa a inuwar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya tona abinda ya hana arewa zaman lafiya.

Tsohon gwamnan Kano ya yi maganganu masu yawa kuma masu muhimmanci a Chatham House a Landan na ƙasar Birtaniya.

Tun kafin gayyatar Kwankwaso, manyan abokan hamayyarsa sun je sun jawabi kan manufofinsu game da neman mulkin Najeriya a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel