Ana Saura ‘Yan Kwanaki Zabe, Rikicin Cikin Gida Yana Wargaza Jam’iyyar APC

Ana Saura ‘Yan Kwanaki Zabe, Rikicin Cikin Gida Yana Wargaza Jam’iyyar APC

  • Muddin ba ayi gyara ba, masu fashin bakin siyasa su na ganin Jam’iyyar APC ta rasa jihar Enugu
  • Akwai yiwuwar Bola Tinubu ba zai tashi da ko 25% na kuri’un Enugu a zaben shugabancin kasa ba
  • Babu jituwa tsakanin manyan ‘ya ‘yan APC da wadanda suke shugabantar jam’iyyar a SWC

Enugu - Yiwuwar samun nasarar jam’iyyar APC a jihar Enugu a 2023 yana kara yin kasa ne kullum a sakamakon wani mummunan rikicin cikin gida.

Punch ta bibiyi sabanin da ake da shi tsakanin jagororin APC a Enugu, ta fahimci cewa har yau rikici bai lafa ba, alhali zabe yana cigaba da karasowa.

Idan aka cigaba da tafiya a haka, ‘dan takaran APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai iya samun cikas a yankin na Ibo a zaben shugabancin kasa.

Kara karanta wannan

Muna Magana da Su – Atiku Ya Kyankyasa Yiwuwar Haduwa da Kwankwaso ko Obi

Kusoshin APC da suka fito daga jihar Enugu, su na zargin Gwamnan Imo, Sanata Hope Uzodinma da yi masu katsalandan da ya jawo hargitswar jam’iyya.

Baya ga David Umahi mai shirin barin gado, Hope Uzodinma ne kadai Gwamna mai-ci da yake mulki a Kudu maso gabashin Najeriya a karkashin APC.

Jiga-jigan APC da suka ja daga

Wadanda ake rigima da su a APC ta reshen Enugu sun hada da tsohon Gwamna, Sullivan Chime, da tsohon shugaban majalisar dokoki, Eugene Odo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jam’iyyar APC
Tinubu yana kamfe a Kwara Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Akwai Ministan harkokin kasar waje, Geoffrey Onyeama, tsohon shugaban APC na jihar, Dr Ben Nwoye da shugaban VON na kasa, Osita Okechukwu.

Za a sauke Ugochukwu Agballah?

A wani korafi da suka aikawa shugabannin jam’iyya na kasa, wadannan ‘yan siyasa sun ce dole ayi maza a dauki mataki a kan shugaban APC na Enugu.

Kara karanta wannan

Wani hanzari: Sirri ya fito, tsohon kakakin majalisa ya ce hadari ne a ba Tinubu ragamar Najeriya

Jiga-jigan APC na reshen jihar Kudu maso gabashin kasar sun ce tun farko, karfa-karfa aka yi har Ugochukwu Agballah ya zama shugaban su a bara.

A wasikar da aka aikawa majalisar NWC, an sanar da ita tun da Cif Agballah ya dare kujera yake barna, yana yakar wadanda suke shugabanni a jam’iyyar.

An bukaci uwar jam’iyya ta tsige Agballah, sannan a nada shugaban rikon kwarya wanda bai cikin ‘yan majalisar gudanarwa na jiha da ke ofis a yanzu.

Wani jagoran jam'iyyar NNPP a yammacin Enugu, Aliyu Adamu ya tabbatar mana da cewa rashin jituwar da aka samu a APC ya raba kan 'yan jam'iyyar.

'Dan adawar ya ce babu abin da ya jawo rikicin cikin gidan illa son dukiya da mukamai. Sai dai bai iya bada tabbacin hakan zai ba NNPP nasara ba.

Inda Maigidana zai maida hankali - Remi Tinubu

Ana da labari matar ‘dan takaran APC a zaben shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta ce gwamnatin mai gidanta za ta fi damuwa kan karfafawa mata da matasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar PDP Ta yi Alla-Wadai Da Rajamun Da Aka Yiwa Shugaba Buhari a Kano

Bayan nan an ji uwargidar Tinubu ta bayyana cewa mai gidanta bai taba matsa mata lamba wajen yin addinta ba, ganin cewa ita kirista ce, shi yana Musulmi

Asali: Legit.ng

Online view pixel