Zaben 2023: Hadimin Buhari Ya Bayyana Hanyar Obi Zai Iya Zama Shugaban Najeriya

Zaben 2023: Hadimin Buhari Ya Bayyana Hanyar Obi Zai Iya Zama Shugaban Najeriya

  • Hadimin shugaban kasa Bashir Ahmed ya ce yana da kwarin gwiwa cewa dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu ne zai ci zaben 2023 kuma ya yi wa'adi biyu
  • Ahmad ya ce lambobin da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour ke cika baki da su ba za su bashi shugabancin kasa ba
  • Mataimaki na musamman din kan sadarwa na zamani ga Shugaba Buhari ya ce Obi ta tafi arewa ya tattauna ya samu shugabancin kasa bayan Tinubu ya yi wa'adinsa biyu

Gidan Gwamnati, Abuja - Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya ce ba ya ganin yiwuwar dan takarar jam'iyyar Labour, Peter Obi, zai iya cin zaben shugaban kasa a 2023.

A wani rubutu da ya yi a Twitter da Legit.ng ta gani a ranar Laraba, 18 ga watan Janairu, mataimakin shugaban kasar na musamman kan sadarwa na zamani ga Shugaba Buhari ya ce lambobin da Obi ke 'cika baki' da su ba za su iya bashi shugabancin kasa ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Tona Asirin Wasu Mutane Dake Fakewa da Addini Don Cimma Burinsu a Najeriya

Obi da Datti
Zaben 2023: Hadimin Buhari Ya Bayyana Hanyar Obi Zai Iya Zama Shugaban Najeriya. Hoto: @PeterObi
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu zai yi wa'adi biyu, in ji Bashir Ahmad

Ahmad, wanda shine mataimakin direkta, ayyuka na musamman kan bangaren watsa labarai, kwamitin kamfen din shugaban kasa na APC, ya cika baki cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar, Ahmed Bola Tinubu, zai yi nasara a zaben da ke tafe.

Ya kuma bayyana kwarin gwiwa cewa Tinubu zai ci zabe karo na biyu a 2027.

Ahmad ya ce Obi ya taho arewa ya tattauna a mara masa baya ya zama shugaban kasa bayan Tinubu ya gama wa'adinsa biyu.

Duk da cewa bai kama sunan Obi ba, martani masu yawa da aka yi kan rubutun ya nuna cewa mutane da dama sun yi imanin yana nufin dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar Labour.

Kazalika, baya ga Tinubu, Obi shine dan takara na biyu cikin manyan yan takara da ya fito daga yankin kudu.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Game Da Rashawa Da Almundahar Kudi Idan Ya Ci Zabe

Ga abin da ya rubuta:

"Ko da ka yarda yanzu ko baka yarda ba, lambobin da ka ke cika baki da su ba za su iya baka shugabancin kasa ba. Bayan Asiwaju ya gama wa'adinsa biyu, za ka iya zuwa arewa ka tattauna kan kujerar. Shi kenan!"

Buhari ya sake bawa tsohon hadiminsa Bashir Ahmad mukami

A baya, shugaba Muhammadu Buhari ya nada tsohon mataimakinsa kan bangaren sada zumunta, Bashir Ahmad a matsayin mataimaki na musamman kan sadarwa na zamani.

Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya ne ya tabbatar da nadin cikin wata takarda na daukan aiki da ya aike wa Bashir a ranar 20 ga watan Yuli.

Asali: Legit.ng

Online view pixel