Zaben 2023: Yaƙin Da APC Da PDP Ke Yi Ya Ɗauki Sabon Salo Yayin Da Tinubu Ya Tona Babban Ajandar Atiku

Zaben 2023: Yaƙin Da APC Da PDP Ke Yi Ya Ɗauki Sabon Salo Yayin Da Tinubu Ya Tona Babban Ajandar Atiku

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben da ke tafe, Bola Tinubu, ya yi zargin Atiku Abubakar na PDP yana da wata ajanda na tallatawa yan Najeriya karerayinsa
  • Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da ya ke kira ga mutanen Jihar Kwara su karbi katinsu na PVC kuma su zabe shi da sauran yan takarar APC a zaben 2023
  • Mai fatan zama shugaban kasar ya ce mutanen jihar Kwara suna jin dadin yanci tun bayan da APC ta karbi mulki daga PDP a jihar a 2019

Ilorin, Kwara - Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben 2023, ya bayyana cewa Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP yana da wata manufar na sayarwa abokansa Najeriya.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin ralli ta kamfen din shugaban kasa a Ilorin, babban birnin jihar Kwara yayin da ya ke kira ga mutanen jihar su zabe shi da sauran yan takarar jam'iyyar APC a zaben da ke tafe a Fabrairun 2023.

Kara karanta wannan

Dino Malaye Yace Ta Karewa Tinubu A Yankinsa Na Kudu Maso Yamma, Tunda Shugabannin Yankin Basa Yinsa

Atiku da Tinubu
Zaben 2023: Yaƙin Da APC Da PDP Ke Yi Ya Ɗauki Sabon Salo Yayin Da Tinubu Ya Tona Babban Ajandar Atiku. Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tinubu ya bayyana hadarin da ke iya faruwa idan an zabe Atiku a 2023

A cikin wata sanarwa da Tunde Rahman na ofishin watsa labarai na Tinubu ya aike wa Legit.ng, mai fatan zama shugaban kasar ya yi kira ga daukakin mutanen jihar Kwara su tabbatar da yancinsu da suka samu shekaru 4 da suka gabata.

Sanarwar ta kara da cewa Tinubu da tawagar kamfen dinsa na shugaban kasa sun cika masarautar makil da magoya bayansu a Metropolitan Square, inda aka yi ralli din.

Saboda yawan al'umma, tsohon gwamnan na jihar Legas ya shafe fiye da awa biyu daga filin jirgin sama na Ilorin kafin ya iso wurin taron.

Abin da ke faruwa a baya-bayan nan game da Bola Tinubu, Atiku Abubakar, PDP, APC, Zaben 2023 a Ilorin

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Game Da Rashawa Da Almundahar Kudi Idan Ya Ci Zabe

Tinubu ya ce mutanen jihar suna jin dadin yanci tun bayan da jam'iyyar APC ta karbi mulki a shekarar 2019, yana mai kira ga gwamnatin Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ta cigaba da yi wa al'umma hidima.

Wani sashi na sanarwar ta ce:

"Dan takarar na jam'iyyar PDP ya yi fice wurin sayar da duk wani abu da ke dauke da sunan Gwamnatin Tarayyar Najeriya a jikinsa. Idan dai dukiyar kasa ne, yana kokarin ganin wata rana ya sayarwa abokan huldarsa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel