Yankin Da Tinubu Ya Fito Sun Masa Tutsu Inji Jam'iyyar Adawa Ta PDP

Yankin Da Tinubu Ya Fito Sun Masa Tutsu Inji Jam'iyyar Adawa Ta PDP

  • Kamfe ya kara daukar dumi, sabida karatowar babban zaben shekarar 2023, inda yan takara shugaban kasa kun karade jihohi sama da goma-goma a Fadin kasa
  • A jihar Ekiti ma dai jam'iyyar PDP ce tai shagube ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC
  • Jam'iyyar PDP tace itace ke tabbacin lashe babban zaben shugaban kasa da za'ai a watan gobe

Ekiti - A wata sanarwa da mai magana da yawun jam'iyyar PDP, Dino Malaye wadda yai mata taken "Masu kula da kafar sadarwa Tinubu sun gaza" ya ce wanda suke kula da hakokin sadarwar Tinubu sun kasa sun koma yarfe da kazafi.

"Duk kararrayin da Tinubu yake na cewa ya riga ya gama da yankin sa na kudu maso yammacin Nigeria, yanzu ta tabbata ba gaskiya bane, sabida yadda jagorori da kuma tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, da wasu kaman Tunde Bakare suka ki mara masa baya"

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Yaƙin Da APC Da PDP Ke Yi Ya Ɗauki Sabon Salo Yayin Da Tinubu Ya Tona Babban Ajandar Atiku

"Mutumin da da ya kasa samun goyan baya a yankinsa, shine zai ce zai bawa wasu ruwa a yankinsu da suka fito, tab! yanzu aka fara wasan." Inji Dino.

Dino ya ci gaba da cewa kwamitin da yake kula da harkokin sadarwa na Tinubu, ya gaza, duk suna tunanin cewa kaman abinda Tinubu yake yi a Lagos shi zai yi a Nigeria, ina! Nigeria ta fi karfinsa. Rahotan Vanguard

"Yadda yan kwamitin yakin neman zabensa suka kasa kare shi da muhimman hujoji wannan yake tabbatar da gazawarsu"
Tinubu/Dino
Yankin Da Tinubu Ya Fito Sun Masa Tutsu Inji Jam'iyyar Adawa Ta PDP Hoto: Vanguard
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A wani labarin da Jaridar AuthorityNews ta rawaito cewa Charles Anuiagwu ya gargadi yan Nigeria kan zabar jam'iyyar APC, yace in ba haka ba zasu zama bayin Jam'iyyar

Aniagwu wanda yake magana a Asaba babban birnin Delta, yace muna roko da kira da yan Nigeria da su dage su watsar da jam'iyyar APC kuma kar su zabe ta a koiwanne mataki.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Game Da Rashawa Da Almundahar Kudi Idan Ya Ci Zabe

Saura kwana talatin da bakwai a gudanar da babban zaben Nigeria

Hukumar zaben Nigeria ta riga ta shirya dan gudanar da babban zaben shekarar 2023, wanda za'ai a watan gobe wato Fabairu.

Za'a gudunar da zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabairun dana yan majalissar dattawa harda na yan majalissar wakilai.

Sai kuma zaben gwamnoni da yan majalissar johohi da za'a gudanar bayan sati biyu da yin zaben shugaban kasa

Asali: Legit.ng

Online view pixel