Maganar Hadin Kan Bola Tinubu da Wata Babbar Jam’iyyar Siyasa Na Daf da Tabbata

Maganar Hadin Kan Bola Tinubu da Wata Babbar Jam’iyyar Siyasa Na Daf da Tabbata

  • Sakataren labarai na Jam’iyyar SDP ya nuna a shirye suke da su hada-kai da APC a zabe mai zuwa
  • Alfa Muhammad ya ce maganar goyon bayan Asiwaju Bola Tinubu tayi nisa, zai yi wahala a fasa ta
  • Akwai ‘yan bangare dabam a jam’iyyar hamayyar da ba su yarda a goyi bayan takarar Tinubu ba

Abuja - Jam’iyyar hamayya ta SDP ta jaddada niyyarta na shiga yarjejeniya da APC mai mulki da ‘dan takaranta na shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu.

Punch ta rahoto jam’iyyar SDP tana mai tabbatar da cewa dunkulewarta da Asiwaju Bola Tinubu yana neman tabbata, kuma zai yi wahala a wargaza shirin.

Wannan jawabi ya fito ne ta bakin Alfa Muhammad wanda shi ne sakataren yada labarai na SDP a ranar Litinin 16 ga watan Junairu 2023, a birnin Abuja.

Kara karanta wannan

Saura Kwana 40 Zabe, Manyan Yan Takara Atiku da Kwankwaso Sun Yi Babban Rashi a Arewacin Najeriya

A cewar Alfa Muhammad, ana daf da cin ma matsaya wajen hada-kai tsakanin bangarensu na SDP da ‘dan takaran APC a zaben shugabancin Najeriya.

Magana tayi nisa a yanzu - SDP

Kakakin na SDP yake cewa babu wanda zai iya takawa lamarin burki domin magana tayi nisa, a cewarsa ba za su iya yi wasa da damar mulkin Tinubu ba.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar Alfa Muhammad, duk wasu shugabannin jam’iyyar SDP na asali sun san da wannan magana, ya nuna wasu daga gefe ne kurum suke yakar shirin.

Bola Tinubu
Bola Tinubu a jirgi Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Nairaland ta rahoto Sakataren yada labaran yana cewa tun shekarar 2020, shugabannin da aka zaba a SDP suka fara tunanin yadda Tinubu zai hau mulki.

Akwai 'yan taware a Jam'iyyarmu - Alfa

Akwai tsagin jam’iyyar adawar da ba su goyon bayan SDP tayi wa ‘dan takaran APC mubaya’a.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamna Ya Gyara Zance, Ya ce Babu Sabani Yanzu Tsakaninsa da Atiku

Mohammed yake cewa wadanda suke adawa da shirin ‘yan bangaren Farfesa Jerry Gana ne da suka shigo jam’iyyar, daga bisani kuma suka koma PDP.

Sakataren labaran SDP na Najeriyan yake cewa tsohon Ministan tarayyar da magoya bayansa sun shigo SDP ne tun farko domin ganin sun karya jam’iyyar.

Jam’iyyar ta ce ‘yan bangaren Gana ba su san komai a kan yadda shugabanci da tsarinsu yake ba.

Manufofin Bola Tinubu

A baya mun rahoto cewa Asiwaju Bola Tinubu ya ce a kwanaki 100 na farko a mulki zai jawo kwararru domin ya canza fasalin tattalin arzikin Najeriya.

Gwamnatin Tinubu za ta taimakawa marasa galihu, a gina gidaje, asibitoci da makarantu, 'dan takaran ya ce zai yi haka ne idan an cire tallafin fetur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel