‘Dan Takarar M/Gwamna Ya Juyawa Jam’iyyarsa Baya, Za a ba Shi Kujera a Mulkin APC

‘Dan Takarar M/Gwamna Ya Juyawa Jam’iyyarsa Baya, Za a ba Shi Kujera a Mulkin APC

  • Kwamred Daniel Obo ya hakura da neman takarar kujerar mataimakin Gwamna a jihar Kuros Riba
  • Shugaban majalisar dokoki ya karbi matashin ‘dan siyasar da wasu mutanensa da suka biyo shi zuwa APC
  • Daniel Obo ya bada sanarwar cewa zai bada karfinsa wajen ganin Jam’iyya mai mulki ta zarce a 2023

Cross River - Daniel Obo ya tattara kayansa ya fice daga jam’iyyar adawa ta SDP alhali shi ne mai takarar kujerar mataimakin Gwamna a jihar Kuros Riba.

A rahoton Premium Times na ya Juma’a, an fahimci cewa shugaban jam’iyyar APC na mazabar Obubra Urban ya karbi Daniel Okpa bayan yi masa rajista.

Da yake jawabi a karshen makon nan, Daniel Okpa ya shaida cewa ba komai ya sa bar SDP zuwa APC ba sai saboda yadda jam’iyyar take tafiya da matasa.

Kara karanta wannan

Dan Takarar Mataimakin Gwamna da Wasu Jiga-Jigai Sun Sauya Sheka Zuwa APC

‘Dan takaran shi ne shugaban majalisar matasa watau NYCN na reshen jihar Kuros Riba.

Okpa ya yaba da aikin Ben Ayade

A cewar Okpa, Gwamnatin Ben Ayade tayi abin a yaba a tsawon shekaru bakwai da tayi a mulki, musamman wajen ba matasa mukamai domin a dama da su.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An rahoto tsohon ‘dan takarar mataimakin gwamnan yana cewa Ben Ayade ya yi kokari wajen rabawa matasa kujeru, ya ce suke rike da 80% na mukamai.

‘Dan Takaran APC
Yakin zaben APC Hoto: www.thisdaylive.com
Asali: UGC

Meyasa Okpa ya tsallako zuwa APC?

Sannan Okpa ya ce ya sauya-sheka daga jam’iyyar SDP mai hamayya ne domin ya taimakawa ‘yan takaran APC mai mulki a wajen ganin sun lashe zabe.

The Cable ta ce Okpa yana ikirarin akwai jagorori 18 na matasa a kananan hukumomin Kuros Riba da suka biyo shi domin ganin APC ta samu nasara.

Kara karanta wannan

Atiku zai tashi a tutar babu a wata jihar da ya saka rai, jiga-jigan PDP sun bi Tinubu

Matashin ya ce akwai fiye da shugabannin mazabu na jam’iyyar SDP tara da suka shigo APC, sannan akwai daruruwan matasa da sun amsa kiran da ya yi.

Za a tafi da Okpa idan an lashe zabe

Shugaban majalisar dokokin jihar Ribas, Eteng Jonah-Williams ya ji dadin yadda Obo ya yi watsi da jam’iyyar SDP, ya tsallako APC a daidai irin wannan lokaci.

Rt. Hon. Eteng Jonah-Williams ya yi wa ‘dan siyasar alkawarin cewa zai samu ‘kujera a gwamnati’, idan APC mai mulki tayi nasarar lashe zabe da za ayi.

NAN ta ce ‘dan majalisar mazabar Boki II, Hilary Bisong ya ce shigowar Obo za ta taimake su.

Hadin gwiwar SDP da APC

Rahoto ya zo kwanaki cewa alamu na kara nuna jam'iyyar APC za ta hada-kai da Jam’iyyar adawa ta SDP domin a dankara su Atiku Abubakar da kasa.

Wani jami’in Jam’iyyar SDP, Alfa Muhammad ya ce tun a shekarar 2020 ake tunanin haduwa da Bola Tinubu, yanzu dama ta samu da su biyu za su dunkule.

Asali: Legit.ng

Online view pixel