2023: Tinubu Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Game Da Rashawa Da Almundahar Kudi Idan Ya Ci Zabe

2023: Tinubu Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Game Da Rashawa Da Almundahar Kudi Idan Ya Ci Zabe

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya isa Kwara yayin da ya ke cigaba da kamfen
  • Tsohon gwamnan na jihar Legas ya fada wa mutanen Kwara cewa idan an zabe shi a 2023, zai share rashawa da sauran nau'ikan almundahar kudi
  • Tinubu ya kuma bukaci magoya bayan jam'iyyar mai mulki a kasa su zabi yan APC daga sama har kasa don su cigaba da samun yancinsu

Kwara - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a ranar Talata ya ce gwamnatinsa za ta magance almundahanar kudi da sauran nau'in rashawa idan an zabe shi.

Dan takarar na APC ya bayyana hakan ne yayin ralli din kamfen dinsa da aka yi a llorin, babban birnin jihar Kwara, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Tona Asirin Manyan Yan Takara Biyu, Yace Hatsari Ne Babba a Zabe Su a 2023

Bola Tinubu
2023: Zan Share Rashawa Da Almundahar Kudi, In Ji Tinubu. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

"Bari in taya ku murna kan samun yanci da kuka yi shekaru hudu da suka shude da muke jadadawa a yau. Idan kuna shirin karfafa yancin ku, ku tafi ku karbi PVC su sake zaben jam'iyyar da yan takararta.
"Tsintsiya alama ce ta yanci kuma da ita za mu share kuma mu cigaba da share rashawa, almundahar kudi, da sauran ababen ki ciki har da rashin tsaro idan an zabe mu.
"A baya an ce muku wannan ba zai faru ba amma gashi kuna ganin shi da idanun ku."

Tinubu: Ku zabi APC daga sama har kasa idan kuna son cigaba da morar yancin ku

Tinubu ya fada wa al'ummar da suka fito taron a Metropolitan Square cewa kada su zabi kowa sai dai shi da sauran yan APC a dukkan zabuka.

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Yi Subul Da Baki A Kogi, Ya Ce A Zabi AP...PDP A Zaben Shugaban Kasa, APC Ta Saki Bidiyon

Ya ce jam'iyyar ta yarda da Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, wanda ya dade yana rikici da Alhaji Lai Mohammed, Ministan Labarai da Al'adu.

Mohammed na cikin jiga-jigan jam'iyyar ta APC ta suka halarci taron yakin neman zaben.

Dubbannin yan jam'iyyar APC sun sauya sheka zuwa PDP a jihar Katsina

A wani rahoton, kun ji cewa mambobin jam'iyyar APC mai mulki a kasa masu yawa a karamar hukumar Ingawa ta jihar Katsina sun koma PDP.

A cewar rahoton Channels TV, lamarin ya faru ne yayin da tawayar kamfen din dan takarar gwamna na PDP a jihar, Yakubu Lado Danmarke, suka yi taro a garin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel