Jam’iyyar APC Ta Dage Taron Gangaminta Na Shugaban Kasa a Jihar Kwara Saboda Dalili

Jam’iyyar APC Ta Dage Taron Gangaminta Na Shugaban Kasa a Jihar Kwara Saboda Dalili

  • Tawagar kamfen Tinubu ta sanar da dage taron gangamin jam’iyyar a jihar Kwara saboda Buhari zai shilla kasar waje ranar Talata
  • Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da APC ta fitar, ta yi karin haske game da dalilin da yasa ta dage taron zuwa gaba
  • Ba wannan ne karon farko da jam’iyyun siyasa ke dage tarukan gangami ba don ba wasu manyan shugabanni damar hakarta

Najeriya - Jam’iyyar APC ta dage taron gangaminta na kamfen din takarar shugaban kasa da ta shirya yi a yau Talata a birnin Ilorin ta jihar Kwara, The Guardian ta ruwaito.

Wannan na zuwa ne a cikin wata sanarwar da kwamitin shirya taron a jihar Kwara ta fitar dauke da sa hannun Saadu Salahu a jiya Litinin 16 ga watan Janairu.

Wannan dage taro dai ya faru ne sakamakon tafiyar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi zuwa wata kasar waje a wannan makon.

APC ta dage taron gangaminta a jihar Kwara
Jam’iyyar APC Ta Dage Taron Gangaminta Na Shugaban Kasa a Jihar Kwara Saboda Dalili | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari na da burin jagorantar gangamin na kamfen Tinubu/Shettima da za a gudanar a birnin Ilorin.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Dalili da yasa aka dage taron gangamin

Wani sashenta ya bayyana cewa:

“Muna bakin sanar da dage taron gangamin kamfen Bola Ahmed Tinubu/Shettima na shugaban kasa a APC da aka shirya yi a Ilorin a ranar Talata, 7 ga watan Janairum 2023. An yi hakan ne don ba shugaban kasa Muhammadu Buhari damar jagorantar taron na kamfen.
“Shugaban kasa yana kan wata tafiyar kasa da kasa ta mako guda a wajen Najeriya, farawa daga ranar Talata, amma ya dage yana son da kansa ya jagoranci gangamin APC a Kwara.”

Ya zuwa yanzu dai ba a bayyana yaushe ne sabon lokaci da ranar da za a gudanar taron na gangami ba, kamar ydda Premium Times ta ruwaito.

Na Fice Daga APC Ne Domin Gujewa Shugabancin Yaudara, Inji Tsohuwar Shugabar Matan Jam'iyyar

A wani labarin, wata jigo kuma shugabar mata a jam'iyyar APC ta ce babu ita babu maganar a APC a yanzu da nan gaba.

Ta ce ta samu matsuguni mai kyau a jam'iyyar APC, don haka ba za ta taba dawowa APC ba.

A cewarta, akwai mayaudara da masu handama da yawa a jam'iyyar APC, musamman a jiharsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel