Ina da Shaidar Cewa Tinubu Dan Ta’adda Ne, Inji Jigon Siyasar PDP Dino Melaye

Ina da Shaidar Cewa Tinubu Dan Ta’adda Ne, Inji Jigon Siyasar PDP Dino Melaye

  • Tawagar dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ta yi martani mai zafi ga 'yan APC a wannan makon
  • APC ta ce, akwai zarge-zarge da yawa game da Atiku, kuma suna da alaka da aikata satar kudin kasa a baya
  • Sai dai, Dino Melaye ya ce, sam bai kamata a saurari APC ba, domin akwai bayanai da ke nuna ta'addanci Tinubu kai tsaye

Najeriya - Kakakin gangamin kamfen takarar shugaban kasa na Atiku Abubakar, Sanata Dino Melaye ya ce akwai shaidu a kasa da ke nuna dan takarar shugaban kasa na APC, Asiwaju Bola Tinubu na da hannu a ta’addanci, Daily Trust ta ruwaito.

Melaye dai na martani ne ga kalaman Mike Achumugu da ya bayyana wasu zarge-zarge kan Atiku a wata hira da gidan talabijin na Channels.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Tona Asirin Manyan Yan Takara Biyu, Yace Hatsari Ne Babba a Zabe Su a 2023

Achimugu ya yi ikrarin a baya shi hadimi ne ga Atiku, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP.

Dino ya yi tonon silili, ya ce Tinubu dan ta'adda ne
Ina da Shaidar Cewa Tinubu Dan Ta’adda Ne, Inji Jigon Siyasar PDP Dino Melaye | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya zargi Atiku da amfani da wasu motoci na musamman domin satar kudade a lokacin da yake mataimakin shugaban kasa ga Obasanjo tsakanin 1999 zuwa 2007.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin PDP ga zargin da take yiwa Atiku na badakala

Sai dai, da yake martani ga maganar, Melaye ya bayyana cewa:

“Atiku Abubakar ba shi ne kadai mataimakin shugaban kasa da aka yi a tarayyar Najeriya ba. Shi ne mutum mafi shuhura a cikin ‘yan Najeriya a duniya baki daya. Mutane na haduwa dashi a titi a kowane lokaci.
“Mun yi yawo a titunan Landan tare dashi. Mutane na tsayar dashi domin daukar hotuna dashi. Don haka, ka ga Atiku, ka dauki hoto dashi, ka yi magana dashi na ‘yan mintuna shikenan ka zama hadiminsa. Wannan bai kama hankali.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Gwamna Ya Gyara Zance, Ya ce Babu Sabani Yanzu Tsakaninsa da Atiku

“Abin da nake fada game da wannan shine: Dukkan abin da wancan yaron ya furta (yana magana kan Mike Achimugu) APC ce ta dauki nauyinsa don kirkirar tsaiko mara dalili. Festus Kayemo ya ma je kotu ya kai kara da sunansa.
“Mutumin da ya kamata ya yi murabus shine mara lafiya. Kundin tsarin mulki ya fadai cewa, kafin ka zama shugaban Najeriya dole ka kasance lafiyayye a kwakwalwa da jiki.

“Tinubu bai da lafiya ta kwakwalwa da jiki. Muna da shaidu kan ta’addancinsa. Muna da shaidun halayensa na banza. Meye yake yi da yake cewa yana son zama shugaban kasa?”

Shugabar matan APC ta sauya sheka

A baya shugabar mata a jam'iyyar APC a jihar Ebonyi ta bayyana ficewa daga APC, ta ce ba za ta sake hada hanya da su Tinubu ba.

A cewarta, sam babu adalai a APC, kuma jam'iyyar na nuna wariya ga tsoffin mambobinta a jihar.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bidiyo ya fito, Atiku ya dawo daga Landan tare da wasu jiga-jigan PDP

A halin da ake ciki, ta zama mamba a jam'iyyar APGA, kuma ta zama mazaunin da ba za ta matsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel