Yan ta'adda
Audu Bulama Bukarti mai rajjin kare hakkin dan Adam ya ce mutanen garin Dansadau da ke jihar Zamfara sun yi bikin wata daya ba tare da harin yan bindiga ba.
Jami'an 'yan sanda da ke sintiri sun kai samame mafakar miyagu da ke kananan hukumomin Birninkudu da Gwaram a jihar Jigawa inda suka yi ram da mutum bakwai.
Wata kungiyar dattawan jihar Zamfara ta koka kan zargin da ta ke na cewa jami'an tsaron jihar suna sakin 'yan bindigan da suka kama da ta'addanci a fadin jihar.
Femi Adesina, mai magana da yawun shugaban kasa, ya ce yana sa ran za a ga bayan manyan 'yan ta'addan kasar nan kafin cikar wa'adin mulkin shugaban kasa Buhari.
Hukumar NSCDC ta tabbatar da damke wasu mutum uku da ta ake zargin 'yan bindiga ne yayin da suka tsere zuwa yankin Magami da ke Zamfara sakamakon ruwan wuta.
Sojojin Najeriya sun yi nasarar fatattakar wasu maharan ISWAP da suka dura yankin. An kama wasu biyar daga cikin 'yan ta'addan tare da hallaka bakwai daga ciki.
Labarin da muke samu da sanyin safiyar nan ta Lahadi na nuna cewa wasu muyagun yan bindiga sun yi awon gaba da babban sarki mai daraja a karamar hukumar Mangu.
Usman Baba, Sifeta janar na ‘yan sanda ya nuna damuwarsa akan yadda mayakan ISWAP su ka harba makamai masu linzami a jihar Borno inda suka yi barna ba kadan ba.
Daya daga cikin shugabannin jam’iyyar APC na jihar Zamfara, Sanata Kabiru Garba Marafa, ya ce ba ya da alaka da gawurtaccen dan bindigan nan,Abdulmuminu Moossa.
Yan ta'adda
Samu kari