Yan bindiga sun bindige tsohuwar shugabar matan PDP, diyarta da wasu mutum biyu

Yan bindiga sun bindige tsohuwar shugabar matan PDP, diyarta da wasu mutum biyu

  • Yan bindiga sun farmaki wata tsohuwar shugabar matan PDP, Ucha Ndukwe a gidanta sannan suka hallaka ta
  • Maharan sun kuma kashe diyar Ndukwa da wasu mutane biyu sannan suka raunata mutum daya
  • Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin

Abia - Wasu tsagerun yan bindiga sun kashe mutane hudu a garin Amangwu da ke karamar hukumar Ohafia ta jihar Abia.

Mutanen da aka kashe sun hada da wata tsohuwar shugabar matan PDP, Ucha Ndukwe, diyarta Chibuzor Ndukwe da kuma wasu mutane biyu, Ndubuisi Ndukwe da Kalu Umah.

Yan bindiga sun bindige tsohuwar shugabar matan PDP, diyarta da wasu mutum biyu
Yan bindiga sun bindige tsohuwar shugabar matan PDP, diyarta da wasu mutum biyu Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Da yake tabbatar da lamarin, shugaban karamar hukumar Ohafia, Dr. Okorafor Ukiwe, ya ce ya kasance a cibiyar lafiya ta tarayya, Umuahia, inda ya je ganin wata da ke kwance a asibiti, itama diya ce ga marigayiyar, Madam Ndukwe, rahoton Nigerian Tribune.

Kara karanta wannan

Abuja: 'Yan bindiga sun hallaka 'yan mata biyu a hanyarsu ta zuwa biki

Ya ce:

“Budurwar ta rasa mahifiya da yar’uwarta wadanda aka harba tare da ita a gidansu.
“An yi mata aiki domin cire harsasan da ke jikinta. Yan bindigar sun kashe mahaifiya da yar’uwarta a gidansu bayan sun kona shagon mahaifiyar tata."

Dalilin da yasa yan bindigar suka kai mata farmaki

Ya ci gaba da bayyana cewa wadanda ake zargin sun fusata cewa matar, wacce ke siyar da abinci tana adawa da ayyukansu a garin, inda ya ce:

“Sun kona shagonta sannan suka je gidanta suka bindige ta kuma da yaranta biyu suka fito, sai yan bindigar suka kuma harbe su.
“Mutum daya ta mutu a nan take yayin da aka gaggauta daukar dayar da ta ji rauni zuwa asibiti kuma tana samun lafiya sosai. Yan bindigar sun kuma kashe wasu maza biyu.”

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki jama'ar gari, sun sace amarya tare da hallaka mutum 8 a Neja

Rundunar yan sandan jihar ta yi martani

Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da cewa an harbe su ne a ranar Talata, rahoton Punch.

Da yake tabbatar da lamarin, jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sandan jihar, Geoffrey Ogbonna, ya ce:

“Mun ji labarin lamarin amma muna jiran rahoto a hukumance domin taimakawa yan sanda sanin cikakken bayanin."

Mazauna sun tsere daga kauyukan Filato yayin da yan bindiga ke tsananta kai hare-hare

A wani labarin, mun ji cewa mazauna kauyuka a karamar hukumar Wase ta jihar Filato sun tsere daga gidajensu yayin da yan bindiga suka tsananta kai hare-hare a yankunan.

Wani mazaunin Anguwan Ali daya daga cikin yankunan da ayyukan yan bindiga ya yawaita, Ibrahim Musa, ya bayyana cewa maharan, sun farmaki kauyen sannan suka ta harbi kan mai uwa da wabi yayin da suke komawa sansaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel