Yan sanda sun kama masu laifi 462, sun kuma kwato makamai

Yan sanda sun kama masu laifi 462, sun kuma kwato makamai

  • Jami'an rundunar yan sandan kasar sun yi nasarar damke mutane 462 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban
  • An damke mutanen ne a cikin watanni biyu da suka gabata a yankuna daban-daban na kasar, an kuma kwato makamai daga hannunsu
  • Har ila yau, an yi nasarar ceto wasu mutane da aka yi garkuwa da su yayin aikin

Rundunar yan sanda ta kama akalla mutane 462 da ake zargi da aikata ta’addanci, kisa, fashi da makami da kuma kungiyoyin asiri.

A cewar rundunar, an kama mutanen ne a cikin watanni biyu da suka gabata a fadin yankuna daban-daban na kasar, Daily Trust ta rahoto.

Yan sanda sun kama masu laifi 462, sun kuma kwato makamai
Yan sanda sun kama masu laifi 462, sun kuma kwato makamai Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Rundunar yan sandan ta kuma bayyana cewa an samo makamai 188, rokoki, harsasai 4,173, motoci uku da babura biyu a cikin lokacin.

Wata sanarwa daga mukaddashin jami’in hulda da jama’a na rundunar, CSP Muyiwa Adejobi, ta ce Sufeto Janar na yan sanda, Usman Baba, ne ya bayyana hakan yayin wata ganawa da shugabannin ‘yan sanda kan yadda jami’an tsaro za su rika gudanar da ayyukansu.

Kara karanta wannan

Ka ba da mu: Rundunar ‘yan sanda ta nemi jami’in da aka ga yana dakon tiren abinci a wurin biki

Ya kara da cewar an ceto mutane 204 da aka yi garkuwa da su a tsakanin lokacin yayin da aka kwato N800,000, kayan sojoji da katan 10 na Pentazocine BP da allurai 30.

A cewar Adejobi, an yi taron ne da nufin sake duba lamarin tsaron cikin gida tare da sake duba dabarun ‘yan sanda wajen tabbatar da tsaron lafiyar jama’a.

Rahoton ya kuma bayyana cewa daga watan Janairun 2022 zuwa yau, baya ga kididdigar ‘Operation Sahara Storm’, an kama wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne su 36, wadanda ake zargi da kisan kai 78, yan fashi da makami 110, masu garkuwa da mutane 50 da kuma ‘yan kungiyar asiri 150 a wasu ayyukan ‘yan sanda a fadin kasar.

Yan bindiga sun bindige tsohuwar shugabar matan PDP, diyarta da wasu mutum biyu

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun kashe 'yan ta'adda sama da 200 a wata jahar arewa

A wani labarin, wasu tsagerun yan bindiga sun kashe mutane hudu a garin Amangwu da ke karamar hukumar Ohafia ta jihar Abia.

Mutanen da aka kashe sun hada da wata tsohuwar shugabar matan PDP, Ucha Ndukwe, diyarta Chibuzor Ndukwe da kuma wasu mutane biyu, Ndubuisi Ndukwe da Kalu Umah.

Da yake tabbatar da lamarin, shugaban karamar hukumar Ohafia, Dr. Okorafor Ukiwe, ya ce ya kasance a cibiyar lafiya ta tarayya, Umuahia, inda ya je ganin wata da ke kwance a asibiti, itama diya ce ga marigayiyar, Madam Ndukwe, rahoton Nigerian Tribune.

Asali: Legit.ng

Online view pixel