Jerin Kasashe 10 Na Duniya Da Suka Fi Fuskantar Ta'addanci A Shekarar 2022, Najeriya Tana Ciki

Jerin Kasashe 10 Na Duniya Da Suka Fi Fuskantar Ta'addanci A Shekarar 2022, Najeriya Tana Ciki

An wallafa manuniyar ta’addanci ta duniya, GTI ta shekarar 2022 wacce ta bayyana yadda ta’addanci da rikice-rikicen kasashen duniya ya kasance.

GTI din da cibiyar tattalin arziki da zaman lafiya, IEP ta wallafa ya nuna yadda ta’addanci ya ke a fadin duniya.

Jerin Kasashe 10 Na Duniya Da Suka Fi Fuskantar Ta'addanci A Shekarar 2022, Najeriya Tana Ciki
Jerin Kasashe 10 Na Duniya Da Suka Fi Fuskantar Ta'addanci A Shekarar 2022, Najeriya Tana Ciki. Photo credit: Audu MARTE /AFP
Asali: Getty Images

Kamar yadda manuniyar ta nuna, Najeriya ce kasa ta 6 wanda hakan ya nuna nasarorin da kasar ta samu na yakar Boko Haram.

Daga zama kasa ta hudu kamar yadda manuniyar ta nuna Najeriya a shekarar 2017, ta koma ta 6 a shekarar nan.

Rahoton ya nuna cewa yawan jama’an da ke rasa rayukan su ya ragu a Najeriya.

Kara karanta wannan

Kamar almara: An haramtawa Magen Rasha shiga kasar wasanni bisa mamayar Ukraine

Kuma ya bayyana nasarar da aka samu bayan halaka shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau da kuma jajircewar gwamnatin tarayya wurin yakar kungiyar.

Jerin kashen guda 10

Kasashe 10 da suka fi fuskantar ta’addanci a shekarar nan:

1. Afghanistan

2. Iraq

3. Somalia

4. Burkina Faso

5. Syria

6. Najeriya

7. Mali

8. Nijar

9. Myanmar

10. Pakistan

An samu sauyi a manuniyar ta’addanci ta duniya, GTI

Rahoton ya nuna yadda matsayin wasu kasashe ya sauya daga inda a baya suke, kamar yadda Burkina Faso ta sha gaban Syria da Najeriya, ta koma matsayi na hudu.

Sannan Pakistan ta koma matsayin na goma inda ta tashi daga ta takwas. Najeriya kuma ta koma ta shida maimakon matsayin ta na hudu a baya.

Har ila yau, idan aka lura da yadda manuniyar ta nuna cikin kasashe 10, ta’addanci ya ragu daga shekarar 2020 zuwa shekarar 2021.

Cikin kasashe 7 da ta’addancin ya ragu, kasar Myanmar ce rikici ya fi raguwa, daga nan sai Jamhuriyar Nijar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel