Zamfara: 'Yan ta'adda sun halaka rayuka 2, sun sace mutum 1, tare da jigata wasu 3

Zamfara: 'Yan ta'adda sun halaka rayuka 2, sun sace mutum 1, tare da jigata wasu 3

  • Miyagun 'yan ta'adda sun kai farmaki anguwar Nasarawa-Burkullu da ke karamar hukumar Bukkuyum ta jihar Zamfara
  • 'Yan ta'addan sun bayyana su hudu a babura 2 inda suka budewa mutane wuta a yammacin Laraba da ta gabata
  • Hatta 'yan sandan yankin sun dinga gudun ceton rai yayin da jama'ar yankin suka dinga kokawa kan yadda masu basu tsaro suke gudu

Zamfara - Tashin hankali ya dawo ga anguwar Nasarawa-Burkullu, yayin da 'yan ta'adda suka kai wa rundunar 'yan sandan farmaki.

Hatsabiban sun yi garkuwa da mutum daya, tare da halaka mutane biyu, sannan suka raunata mutane uku yayin kai harin misalin karfe 6:50 na yamma, a ranar 2 ga watan Maris, 2022.

Anguwan Nasarawa-Burkullu na cikin karamar hukumar Bukkuyum dake jihar Zamfara, a arewa maso yammacin Najeriya, HumAngle ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mazauna sun tsere daga kauyukan Filato yayin da yan bindiga ke tsananta kai hare-hare

Zamfara: 'Yan ta'adda sun halaka rayuka 2, sun sace mutum 1, tare da jigata wasu 3
Zamfara: 'Yan ta'adda sun halaka rayuka 2, sun sace mutum 1, tare da jigata wasu 3. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

A hari na karshe da aka kai wa yankin, a ranar 15 ga watan Disamba 2021, miyagun sun yi garkuwa da mazauna anguwan guda 30.

A lokacin da aka kai wannan farmakin na ranar Laraba, tawagar 'yan ta'addan sun auka anguwar kimanin minti 10 bayan kiran sallar magriba, inda suka doshi sansanin rundunar 'yan sandan Najeriya da harbi ba kakkautawa, hakan ya sa mazauna yankin tserewa.

HumAngle ta ruwaito cewa, an harbi wani mai gyaran takalmi, Nuhu Anas, mai shekaru 23 a wuya, da kuma wani matashi mai shekaru 21 dan gidan Alhaji Surajo a kai. A take dukkan su suka rasa rayukan su.

An garzaya da wadanda suka samu rauni asibitin Nasarawa, inda suke samun kulawa. Sai dai, har yanzu mazauna yankin ba su ji komai game da wadanda aka yi garkuwan dasu ba.

Kara karanta wannan

Zamfara: Yan bindiga sun bude wa juna wuta a kasuwa, rayuka da dama sun salwanta

Ganau, wanda ya bukaci a sakaya sunan sa, ya ce, "Muna tare da kusan 'yan sanda guda biyar duk da DPO jim kadan bayan idar da sallar magriba, lokacin da muka fara jin karar harbin bindiga na karato ofishin 'yan sanda."
"Kafin kace kwabo, dukkan mu mun tsere don ceton rayuwarmu. Wasu daga cikin mu sun fada gidajen makwabta. Maganar gaskiya, ban lura ni da DPO mun fada cikin bayi ba, gami da kwantawa don kaucewa harsashin da suke harbawa."
"Yayin da suke harba alburusai daga wajen Nasarawa zuwa cikin anguwan, 'yan bindiga sun saci hanya zuwa babban birnin, har sai da suka isa dai-dai kofar shagon Alhaji Surajo, wanda ke cikin kasuwa, inda suka yi ta harbi a iska," a cewar Kabiru Sani, mai shekaru 29, wani mazaunin yankin.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun yi kokarin siffanta yanayin harin da ayyukan 'yan ta'addan.

Wani mazaunin yankin, Murtala Tabalaya ya ce, "'Yan bindigan basu wuce su hudu ba, sanye da 'jallabiya' kamar Larabawa. Suna rike da bindigogi, yayin da suka shigo cikin garin kan babura biyu. Sun halaka mutanen da ba su ji ba basu gani ba guda biyu, bayan raunata mutane uku, daga bisani suka yi garkuwa da daya daga cikin masu tsaron shagon Alhaji Surajo "

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan ta’addan sun yi garkuwa da malamin addini da wasu mutum 7 a jihar Neja

Mazauna yankin sun koka game da yadda jami'an tsaron suka nuna halin ko in kula a kan lamarin, hakan yasa Alhaji Hamisu Ibrahim yin tsokaci cikin rashin jin dadi:

"Babu wani jami'in tsaron da ya iya kawo wa mazauna yankin wani dauki a lokacin da kuma bayan aukuwar lamarin."

An kuma: 'Yan ta'adda sun kai farmaki Zamfara, sun sheke rayuka 18

A wani labari na daban, a kalla rayuka 18 ne suka salwanta yayin da wasu masu yawa suka raunata bayan farmakin 'yan ta'adda a Kadaddaba da ke karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara.

Premium Times ta ruwaito cewa, farmakin ya kwashe kusan sa'o'i hudu tunda 'yan ta'addan sun bayyana wurin karfe goma na dare ne kuma suka kai har hudun asuba kuma shi ne na farko da aka taba kai wa kauyen.

Kilomita kadan ke tsakanin kauyen Kadaddaba da kwalejin gwamnatin tarayya ta Anka, wacce ba ta da nisa da garin Anka.

Kara karanta wannan

Borno: Mayakan ta'addancin ISWAP sun sheke rayuka 5 Kautikari a sabon hari

'Yan ta'adda sun sha kai farmaki kauyukan yankin inda suke sace mutane sai an biya kudin fansa tare da satar shanu na tsawon shekaru a yankunan arewa maso yammacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel