Mutum 8 Sun Tsara Kashe Trump, Netanyahu da Harba Bama Bamai a Amurka
- Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta kai karar mutum takwas da ake zargi da shirya kashe Shugaba Trump da mataimakinsa, JD Vance
- Binciken FBI ya nuna makircin ya hada da amfani da jiragen sama marasa matuka dauke da bama-bamai da kuma 'yan bindiga a White House
- Gwamnatin Amurka ta ce an kama dukkan mutane takwasda ake zargi tun kafin su kai harin, shekarunsu kuma sun kai tsakanin 19 zuwa 32
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington - Ma'aikatar shari'ar Amurka ta gabatar da tuhume-tuhume kan mutum takwas da ake zargi da shirya kai hari kan shugaba Donald Trump da mataimakin shi JD Vance da kuma wasu manyan jami'an gwamnati.
Alkalin kotun Amurka ya fara sauraron karar bayan hukumomin tsaro sun ce sun katse makircin tun kafin a gama kulla shi, kuma duk masu laifin sun riga sun kasance a hannun hukuma.

Source: Getty Images
Rahoton da Reuters ta wallafa ya bayyana cewa shekarun wadanda ake tuhuma ba su wuce tsakanin shekaru 19 zuwa 32 da haihuwa ba.
Abin da Makircin Ya Kunsa
Binciken da FBI ta gudanar ya nuna wadanda ake tuhuma sun tsara jerin sunayen mutanen da suke so su kashe, ciki har da shugaba Trump, mataimakinsa, Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Labarin da Roya News ta wallafa ya nuna cewa attajirin Amurka, Elon Musk, da sauran manyan jami'an gwamnati na cikin wadanda ake zargin za a farmaka.
An ce makircinsu shi ne su kai hari a lokacin wani taron kokawa na Mixed Martial Arts da aka yi a fadar White House, wanda ya yi daidai da ranar haihuwar Trump da kuma cika shekaru 250 na 'yancin Amurka.
Rahotanni sun nuna cewa Donald Trump da 'yan majalisa da wasu daga cikin hadimansa sun halalara wajen taron, amma Netanyahu bai je ba.
Yadda aka tsara kashe Trump
Hukumomin tsaro sun bayyana cewa makircin ya hada da amfani da jiragen sama marasa matuka dauke da bama-bamai, da za a harba zuwa bangaren Arewacin fadar White House.
An ce manufar harin na farko shi ne ya tarwatsa taron ya sa mutane gudu ta wata ƙofar fita ta musamman. A nan ne ake zargin mutanen sun shirya su bude wuta ga duk wanda ya gudu.
Hukumomi kuma sun ce makircin ya kunshi tarurrukan sirri da aka gudanar ta hanyar manhajojin sadarwa na intanet.

Source: Getty Images
Tuhumar da ake wa wadanda aka kama sun hada da makircin bayar da tallafi ga masu ta da zaune tsaye da kuma makircin shirya kashe jami'an gwamnati.
Isra'ila ta kama dan Amurka
A wani labarin, mun kawo muku cewa cewa gwamnatin Benjamin Netanyahu ta kama wani matashi dan asalin kasar Amurka kan zargin leken asiri.
Gwamnatin kasar Isra'ila ta zargi matashin da tattara hotuna da wasu abubuwan sirri a wurare daban-daban na kasar domin bai wa Iran da suke takun saka.
Rundunar 'yan sandan Isra'ila ta ce za a gurfanar da matashin bisa zarge-zargen da aka masa, inda ya kasance dan Amurka na farko da aka yi wa irin zargin.
Asali: Legit.ng

