Yaki da 'Yan Bindiga: Tinubu Ya Zauna da Hafsoshin Soji, Jami'an Leken Asiri

Yaki da 'Yan Bindiga: Tinubu Ya Zauna da Hafsoshin Soji, Jami'an Leken Asiri

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi babban taron tsaro da shugabannin rundunar soji da hukumomin leken asiri a fadar shugaban kasa ranar Alhamis
  • Taron ya zo ne bayan dakarun Najeriya sun hallaka 'yan ta'adda kusan 300 a jihohin Zamfara da Katsina tare da kashe wani babban kwamandan 'yan bindiga
  • Haka kuma ya zo bayan an kai wa sansanin soja na Mairari hari a Arewa maso Gabas, kuma an kai fiye da hare-hare 13 kan sansanonin soja a 2026 kadai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya tara manyan hafsosin rundunar soji, shugabannin hukumomin leken asiri da masu ba shi shawara kan tsaro a fadar shugaban kasa da ke Abuja ranar Alhamis da maraice.

Taron ya dauki fiye da awowi biyu ana tattaunawa kan halin tsaro a fadin kasar da kuma ayyukan soji a yankuna daban-daban.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 19 da manyan sarakunan Arewa sun cimma matsaya kan kafa yan sandan jihohi

Shugaban kasa da hafsoshin tsaro
Shugaba Bola Tinubu da hafsoshin tsaro. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Wadanda suka halarci zaman

Punch ta rahoto cewa daga cikin wadanda suka halarta akwai Babban Mai Shawara kan Tsaron Kasa, Nuhu Ribadu; Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa; Babban Hafsan Sojan Najeriya, Janar Olufemi Oluyede.

Shugaban Sojan Kasa, Laftanal Janar Waidi Shuaibu da Shugaban Leken Asiril Soji, Laftanal Janar Emmanuel Undiandeye sun hallara.

Haka kuma, Darakta Janar na DSS, Adeola Ajayi; Darakta Janar na Hukumar Lekon Asirin Kasa, Mohammed Mohammed;ya halarci zaman.

Suefto Janar na 'Yan Sanda, Tunji Disu da sauransu duk sun kasance a wajen taron tare da sauran wakilan hukumomin tsaro.

Harin da aka kai kafin taron

Vanguard ta wallafa cewa taron ya zo ne kwana biyu bayan dakarun Operation Fansan Yamma sun yi nasara wajen dakile wani yunkurin 'yan ta'adda a jihohin Zamfara da Katsina.

A ranar 7 ga watan Yulin 2026, jiragen sama guda uku na sojan sama suka bi sawun ayarin babura kusan 300 na masu dakon makamai da suka fito daga yankin Sunke-Kumbo suka nufi Gummi, kuma aka kaddamar da hare-hare da suka tarwatsa su.

Kara karanta wannan

Tsaro: Sarkin Musulmi ya tara malaman Izala, Darika da sarakuna a Kaduna

Baya ga haka, a wani aiki daban, dakarun sun kashe Alhaji Tukur wanda soji suka bayyana shi a matsayin wani babban kwamandan 'yan bindiga kuma kanin dan fashi, Alhaji Shehu Bagiwaye, a Dogon Kade.

Waidi Shuaibu a wajen taron sojoji
Hafsun sojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shuaibu. Hoto: HQ Nigerian Army
Source: Facebook

A Arewa maso gabas, dakarun Operation Hadin Kai sun kare sansanin soja na Mairari daga wani sabon farmaki da aka kai ranar 1 ga Yulin 2026.

A lokacin da aka wallafa wannan rahoto, fadar shugaban kasa ba ta fitar da wata sanarwa dauke da cikakken bayani kan abin da aka tattauna a taron ba.

An saye motocin yaki a Sokoto

A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin jihar Sokoto ta kaddamar da motocin sulke, babura da sauran kayan yaki da 'yan ta'adda.

An gudanar da taron raba kayayyakin ne a Sokoto, inda gwamnatin Gwamna Ahmad Aliyu ta ce ta kashe sama da Naira biliyan 20 wajen sayen kayan fadan.

Manyan mutane daga ciki da wajen jihar sun hallara wajen raba kayayyakin, inda ministan tsaro, Christopher Musa ya ce matakin zai kara karfafa hukumomin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng