Kashe-kashen Kebbi: Ku ragargaji 'yan bindiga kafin su kai hari, Buhari ga jami'an tsaro

Kashe-kashen Kebbi: Ku ragargaji 'yan bindiga kafin su kai hari, Buhari ga jami'an tsaro

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci jami'an tsaro da su ragargaji 'yan bindiga kafin su kai hari
  • Buhari ya yi wannan kira ne yayin da yake mika ta'aziyya ga iyalan yan sa kai sama da 60 da yan bindiga suka kashe a jihar Kebbi
  • Shugaban kasar ya bayyana harin a matsayin zalunci kuma mai gigitarwa

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga jami'an tsaro da su kara kaimi da rubanya kokarinsu domin dakile shirin yan ta’adda tun kafin su kai ga kaddamar da hare-hare.

Buhari ya yi wannann kiran ne yayin da yake nuna bakin ciki kan abun da ya kira da “mummunan kisan gillar da yan bindiga suka yiwa yan sa kai da dama yayin da suka yi masu kwanton bauna a karamar hukumar Sakaba/Wassagu.”

Kara karanta wannan

An damke dan sandan bogi yana amfani da kayan sarki wajen damfarar mutane

Kashe-kashen Kebbi: Ku ragargaji 'yan bindiga kafin su kai hari, Buhari ga jami'an tsaro
Kashe-kashen Kebbi: Ku ragargaji 'yan bindiga kafin su kai hari, Buhari ga jami'an tsaro Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

A cewarsa:

“Irin wannan babban ta’asar yana da gigitarwa kuma ina son ba yan Najeriya tabbacin cewa zan yi iya bakin kokarina wajen magance wannan mummunan abu da gaske.
“Babban damuwata shine barazana ga rayuwa da wadannan gungun makasan ke yi da kuma daukar rai da suke yi ba a bakin komai ba.”

Shugaba Buhari a cikin wata sanarwa da kakakinsa, Mallam Garba Shehu, ya fitar, ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan mamatan da lamarin ya ritsa da su.

Shugaban kasar ya kara da cewa:

"Yayin da nake mika ta'aziyyata ga iyalan wadanda aka yiwa wannan zaluncin, bari na yi amfani da wannan damar wajen sake kira ga jami'an tsaronmu da suka kara kaimi da rubanya kokarinsu domin dakile shirin yan ta'addan tun kafin ma su kai hare-haren."

Kara karanta wannan

Birbishin rikici a Pleateau yayinda aka hallaka Shanu 100 ba gaira ba dalili

Tashin Hankali: Yan bindiga sun bindige Yan Sa'kai sama da 60 a jihar Kebbi

Da farko dai mun ji cewa yan Bijilanti, waɗan da aka fi sani da yan Sa'kai aƙalla mutum 63 suka rasa rayuwarsu a hannun yan bindiga a jihar Kebbi.

Daily Trust ta rahoto cewa, mummunan lamarin ya auku ne bayan jami'an Sa'kai sun kaddamar da yaƙi da yan ta'addan a yankin masarautar Zuru a jihar Kebbi.

A halin yanzun an gudanar da jana'izar waɗan da lamarin ya faɗa kan su, kuma lamarin ya auku ne da tsakar daren ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel