Rundunar yan sanda ta kame yan ta'adda 36 da wasu mutum 388 cikin watanni biyu

Rundunar yan sanda ta kame yan ta'adda 36 da wasu mutum 388 cikin watanni biyu

  • Rundunar yan sandan ƙasar nan ta sanar da dumbin nasarorin da jami'anta suka samu a fadin Najeriya cikin watanni biyu
  • Sufetan yan sanda, IGP Usman Alkali Baba, ya ce dakaru sun kama yan ta'adda 36, da wasu masu aikata manyan laifuka 388
  • Ya ce daga cikin waɗan da aka kama akwai masu garkuwa, fashi da makami, yan kungiyar Asiri da sauran su

Abuja - Hukumar yan sandan ƙasar nan ta sanar da cewa dakarunta sun kame mutum 36 dake da hannu a ayyukan ta'addanci cikin watanni biyu, kamar yadda The Nation ta rahoto.

Yan sandan sun kuma kama wasu 388 bisa zargin aikata kisan kai, fashi da makami, garkuwa da mutane, da yan asiri cikin wata biyu.

Sufetan yan sandan ƙasa, IGP Usman Baba, shi ne ya bayyana haka a Abuja, yayin taronsa da mataimakan sufeta janar da Kwamishinonin yan sanda.

Kara karanta wannan

Birbishin rikici a Pleateau yayinda aka hallaka Shanu 100 ba gaira ba dalili

Bajen yan sanda
Rundunar yan sanda ta kame yan ta'adda 36 da wasu mutum 388 cikin watanni biyu Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ya ce dakarun yan sanda sun kama mutanen da ake zargi ne a Operation daban-daban da suka kaddamar a faɗin Najeriya.

Sufeto na ƙasa ya ce an kama mutum 78 da zargin aikata kisa, yan fashi da makami 110, masu garkuwa 50 da kuma yan kungiyar asiri 150.

Yan sanda sun ceto mutane

Baba yace yan sanda sun ceto mutum 204 da akai garkuwa da su, yayin da suka kwato makamai 55 kala daban-daban da kuma alburusai 1,561 cikin wannan lokacin.

Sufetan yan sanda ya ce:

"Dakarun Operation Sahara Storm da aka kaddamar a jihar Sokoto sun samu nasarori da dama. An kafa dakarun ne domin gano maɓoyar yan bindiga a Gudugudu, jejin Tarke da sauran wurare."

A wani labarin kuma Matar Abdulmalik Tanko ta ba da shaida a Kotu kan kisan Hanifa Abubakar

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama masu laifi 462, sun kuma kwato makamai

Matar wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar, Jamila Muhammad, ta ba da shaida a Kotu bayan ya ce ba shi ya kashe ta ba.

Jamila ta faɗi yadda ya kawo mata yarinyar da kuma karyar da ya mata game da ita, har zuwa ranar da ya ɗauke ta da daddare bayan kwana 5.

Asali: Legit.ng

Online view pixel