Jami'an tsaro sun kashe 'yan ta'adda sama da 200 a wata jahar arewa

Jami'an tsaro sun kashe 'yan ta'adda sama da 200 a wata jahar arewa

  • Jami'an tsaro sun yi gagarumin nasara kan yan ta'adda a jihar Neja inda suka kashe sama da guda 200 cikin kwanaki hudu
  • An ragargaji yan ta'addan ne a kananan hukumomin Mariga, Wushishi, Mokwa da Lavun da ke jihar
  • Kwamishinan kananan hukumomi, harkokin sarauta da tsaron cikin gida, Emmanuel Umar, ya tabbatar da hakan, inda ya ce sun sauya dabaru don kawar da miyagu a jihar

Niger - Jami’an tsaro a jihar Neja sun kashe yan ta’adda sama da guda 200 a cikin kwanaki hudu da suka gabata.

The Nation ta rahoto cewa an kashe yan ta’addan ne a kananan hukumomin Mariga, Wushishi, Mokwa da Lavun.

Jami'an tsaro sun kashe 'yan ta'adda sama da 200 a wata jahar arewa
Jami'an tsaro sun kashe 'yan ta'adda sama da 200 a wata jahar Neja Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Kwamishinan kananan hukumomi, harkokin sarauta da tsaron cikin gida, Emmanuel Umar, wanda ya bayyana hakan a yayin wani taro kan lamarin tsaro a jihar ya ce kungiyoyin yan bindiga hudu na ta kai farmaki a jihar, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Babu dadi: IGP ya koka kan yadda 'yan sanda ke amfani da makamai ta wasu hanyoyi

Ya ce yan ta’adda da dama sun tsere da raunukan harbi, inda ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da bayanan sirri domin ba hukumomi damar yin nasara a yaki da rashin tsaro da ke gudana a yanzu.

Umar ya bayar da sunayen kungiyoyin yan ta’addan a matsayin; kungiyoyin ta’addanci na Bello Turji, Yellow Janbros, Kachalla Halilu da Ali Kawaje.

Ya ci gaba da fadin cewa jami’an tsaro biyu sun mutu a yayin arangama da yan fashin.

Kwamishinan ya ce an kwato babura da dobbobi da dama, hakazalika an samo bindigogi daga hannunsu a yayin arangamar. Ya ce jahar ta sake dabaru sannan kuma a shirye take ta kawo karshen ta’addanci.

Umar ya yaba wa jami’an tsaro, al’umman gari da masarautun gargajiya da kuma kafofin watsa labarai a kan goyon bayan da suke bayarwa a yaki da ta’addanci da ke gudana a jihar.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Yan ta’addan sun yi garkuwa da malamin addini da wasu mutum 7 a jihar Neja

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki jama'ar gari, sun sace amarya tare da hallaka mutum 8 a Neja

A wani labarin, mun kawo a baya cewa Yan bindiga da yawansu ya kai 100 sun farmaki wasu garuruwa a karamar hukumar Lavun da ke jihar Neja.

An tattaro cewar yan bindigar sun kai hari wajen wani taro na aure sannan suka sace amarya. Sun kuma kashe mutane takwas sannan suka jikkata wasu da dama.

Garuruwan da aka kai hari sun hada da Egbako, Ndaruka, Ebbo, Ndagbegi, Tshogi, Gogata da Ndakogitu, rahoton Arise tv.

Asali: Legit.ng

Online view pixel