Mazauna sun tsere daga kauyukan Filato yayin da yan bindiga ke tsananta kai hare-hare

Mazauna sun tsere daga kauyukan Filato yayin da yan bindiga ke tsananta kai hare-hare

  • Jama'a sun tsere daga gidajensu a kauyukan da ke karamar hukumar Wase ta jihar Filato sakamakon yawan hare-haren da yan bindiga ke kaiwa
  • Maharan sun farmaki kauyen Anguwan Ali inda suka bude wuta kan al'umma, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da yawa
  • Hakazalika ana zaman dar-dar a garin Bunyun sakamakon hare-haren miyagun

Plateau - Daily Trust ta rahoto cewa mazauna kauyuka a karamar hukumar Wase ta jihar Filato sun tsere daga gidajensu yayin da yan bindiga suka tsananta kai hare-hare a yankunan.

Halin da ake ciki a garuruwan Anguwan Ali da Bunyun

Wani mazaunin Anguwan Ali daya daga cikin yankunan da ayyukan yan bindiga ya yawaita, Ibrahim Musa, ya bayyana cewa maharan, sun farmaki kauyen sannan suka ta harbi kan mai uwa da wabi yayin da suke komawa sansaninsu.

Kara karanta wannan

Zamfara: Yan bindiga sun bude wa juna wuta a kasuwa, rayuka da dama sun salwanta

Ya ce:

“A ranar Lahadi, sun farmaki Anguwan Ali lokacin da yan bindgar ke komawa sansaninsu. Sun harbi mutane da yawa kuma da dama sun mutu. A kan idona aka harbi wani. Mazauna kauyen da dama sun tsere da raunin harbi."
Mazauna sun tsere daga kauyukan Filato yayin da yan bindiga ke tsananta kai hare-hare
Mazauna sun tsere daga kauyukan Filato yayin da yan bindiga ke tsananta kai hare-hare Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wani mazaunin garin Bunyun, Abduhamid Cikaiki, ya kuma fada ma Daily Trust cewa suna zaman dar-dar a kauyukansu sannan suna kira ga gwamnatocin tarayya da na jiha a kan su kawo masu dauki domin babu jami’an tsaro a garin nasu.

An tura jami'an tsaro kauyukan

Kakakin Operation Safe Haven da ke tabbatar da zaman lafiya a jihar, Manjo Ishaku Takwa, ya ce akwai jami’ai a kauyukan da ke Wase tun a ranar Talata, inda suke aikin kakkaba domin yakar yan ta’addan.

Don haka, ya roki mutane da su taimakawa jami’an da bayanai masu amfani wanda zai taimaka a yakin da suke yi.

Kara karanta wannan

Jakadan Canada a Najeriya ya ziyarci marasa gata a kasan gada, hotunansu suna wasa sun taba zukata

Zamfara: Yan bindiga sun kaure da fada tsakanin su kan dabbobi, sun yi wa juna barna

A gefe guda, musayar wuta ya barke ranar Litinin tsakanin tawagar yan bindiga dake hamayya da juna a kusa da ƙauyen Kunchin Kalgo, karamar hukumar Tsafe, jihar Zamfara.

Wani mazaunin yankin, Sani Usman, ya shaida wa Daily Trust cewa yan bindigan sun gwabza tsakaninsu ne kan sabanin da ya shiga game da rabon shanun da suka sato.

A kwanakin baya, mutane sun ga wasu tawagar yan bindiga ɗauke da makamai a kan babura a ƙauyen Kunchin Kalgo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel