ISWAP na horar da masu kunar bakin wake domin kai wa hukumomin tsaro hari, DSS

ISWAP na horar da masu kunar bakin wake domin kai wa hukumomin tsaro hari, DSS

  • Hukumar tsaro ta farin kaya ta fallasa yadda mayakan ISWAP ke horar da kwararru domin kunar bakin wake
  • Binciken hukumar yaa bankado cewa, miyagun za a tura su ne hukumomin tsaro domin kai miyaagun farmaki
  • Hukumar tsaron ta farin kaya ta ce harin da miyagun ke kaiwa ya ragu a shiyyar arewa maso gabas, amma ya zama dole a kara kiyayewa

Bayan wani binciken sirri da hukumar tsaron farin kaya tayi, ta ce ta gano yadda mayakan ISWAP ke horar da masu kunar bakin wake yadda za su kai hari ga jami'an tsaro da yankunan kasar nan.

Haka zalika, DSS ta bayyana yadda wasu daga cikin ISGS dake yankin tafkin Cadi, wadanda suka yi hijira zuwa Mali, bayan takura musu da sojojin da rasha tayi haya suka yi, inda suka shigo kasar Najeriya don karfafa ayyukan yan ta'addan ISWAP, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Mamayar Rasha: Mutane miliyan 1 sun yi gudun hijira a Ukraine cikin mako 1, UNHCR

ISWAP na horar da masu kunar bakin wake domin kai wa hukumomin tsaro hari, DSS
ISWAP na horar da masu kunar bakin wake domin kai wa hukumomin tsaro hari, DSS. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Shugaban SDES na jihohin arewa maso gabas, Babagana Bulama, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Hukumar ta hada taron, domin ta duba kalubalen dake tunkaro yankin, TheCable ta ruwaito.

Bulama, wanda kuma shi ne daraktan DSS a jihar Adamawa, ya bayyana yadda shiyyar arewa maso gabas ke cigaba da fuskantar kalubalen tsaro iri-iri.

"Manya daga cikin matsalar tsaron da shiyyar nan ke fuskanta shi ne yadda Boko Haram da ISWAP suke cin karen su ba babbaka a shiyyar.
"Duk da ire-iren hare-hare da 'yan ta'addan ke kaiwa ya ragu cikin kwanakin nan, lokacin da jami'an tsaro suke dakile ta'addanci, bayanan sirri sun nuna yadda ISWAP ke horar da masu kunar bakin wake da shirin kai farmaki ga jami'an tsaro da yankunan da suke yawan kai hari," yace.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari: Zaben 2023 zai fi kowane zabe zama sahihi saboda kokarin Buhari

Bulama ya cigaba da fallasa yadda masu garkuwa da mutane da 'yan bindiga suka mayar da tarin wuraren da ba mutane, musamman tsaunuka da dajika a jihohin shiyyar, a matsayin maboya, inda suke cin karen su ba babbaka.

Ya kara da cewa: "Bincike ya nuna yadda wasu daga cikin wadannan hatsabiban suka zo daga arewa maso yamma da tsakiyar shiyyoyin arewa, inda jami'an tsaro ke fattatakar su."

Bulama ya ce, an samu saukin rikicin manoma da makiyaya cikin lokutan nan, saboda karasa girbi da manoma suka yi.

Rikici ya kai ga sojoji kashe jami'in tsaron farin kasa na DSS a cikin wani otal

A wani labari na daban, rahoto daga Daily Trust ya ce, wasu sojoji uku sun kashe wani jami'in hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) a wani otal da ke Ado-Ekiti.

Sojojin sun mamaye otal din ne da misalin karfe 7:30 na yammacin ranar Alhamis inda daya daga cikin sojojin ya dabawa jami’in DSS din wuka har lahira.

Kara karanta wannan

2023: Tsohon Shugaban Banki, Hayatu-Deen, Ya Shiga Jerin Masu Neman Gadon Kujerar Buhari

Karin bayanin da aka tattara ya nuna cewa lamarin ya faru ne sakamakon takaddama tsakanin sojoji da jami'in na DSS, bayan cafke wani matashi da ake zargi da aikata damfara ta yanar gizo a cikin otal din.

Asali: Legit.ng

Online view pixel