Tambuwal ya bayyana irin gwagwarmayar da yake sha da rashin tsaro a jiharsa

Tambuwal ya bayyana irin gwagwarmayar da yake sha da rashin tsaro a jiharsa

  • Aminu Waziri Tambuwal, gwamnan jihar Sokoto ya sanar da gwagwarmayar da yake yi a kan rashin tsaron jiharsa
  • Ya sanar da cewa samar da tsaro hakkin gwamnatin tarayya ne amma ya na kokarin tallafawa hukumomin tsaro a jihar
  • Ya ce yana gyara da gina sabbin ofisoshin 'yan sanda kuma ya samarwa sojoji jirage marasa matuka tare da bayanan sirri

Sokoto - Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya bayar da labarin yadda jiharsa ke gwagwarmaya da rashin tsaro inda yace mulkinsa na samar da dukkan goyon baya da taimako ga hukumomin tsaro domin inganta ayyukansu na bai wa jama'ar jihar tsaro.

Vanguard ta ruwaito cewa, Tambuwal ya sanar da manema labarai a Sokoto cewa, duk da matsalolin tsaro hakkin gwamnatin tarayya ne, gwamnatin jihar na samar da goyon baya da taimako ga hukumomin tsaro.

Kara karanta wannan

Yajin aiki a Jami'o'i: Abubuwan da aka tattauna tsakanin ASUU da FG a taron yau Talata

Tambuwal ya bayyana irin gwagwarmayar da yake sha da rashin tsaro a jiharsa
Tambuwal ya bayyana irin gwagwarmayar da yake sha da rashin tsaro a jiharsa. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya ce wannan goyon bayan ya hada da samarwa hukumomin tsaro kayan aiki, ababen hawa da alawus din ayyuka na musamman a jihar.

“Babu abinda hukumomin tsaro a Sokoto ke bukata daga wurinmu ta fannin tallafi da ba mu samar musu. A shekaru hudu zuwa biyar da suka gabata, mun samar da ababen hawa 500 ga jami'an tsaro a jihar Sokoto.
"Kamar yadda nake fadi yanzu, mun biya dukkan alawus babu mai bin mu bashi. A duk lokacin da za su yi aiki, muna basu goyon baya. Muna basu alawus a kowanne wata. Muna yin iyakar kokarinmu kuma za ku iya tabbatar da ikirarinmu.
"Muna gini kuma muna gina sabbin ofisoshin 'yan sanda kuma muna gyaran sauran. A halin yanzu, idan mun kammala gyaran za mu gina wasu sabbi a jihar," Tambuwal yace.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya gana da daliban jihar Sokoto da ke Ukraine, ya bukaci iyaye da su kwantar da hankalinsu

Tambuwal ya kara da cewa jihar ta na tallafawa hukumomin tsaron wurin tattaro bayanan sirri kuma suna tabbatar da cewa ana amfani da kayayyakin da suka dace wurin bai wa jama'a kariya.

“Muna bai wa sojoji tallafi wurin samar musu da jirage marasa matuka, kuma muna yin hakan ga hukumar tsaron farin kaya."

Gwamnan ya bayyana cewa, daga cikin kokarinsu na inganta tsaron jihar, gwamnatin Sokoto ta samar da rijistar mazauna gidan haya domin daukan bayanan dukkan masu zama a cikin jihar.

Vanguard ta ruwaito cewa, idan ta fara aiki, hukumar za ta taka rawar gani wurin inganta tsaron jihar.

El-Rufai ya fallasa alakar da gwamnati ta gano tsakanin 'yan sanda, sojoji da 'yan bindigan Najeriya

A wani labari na daban, Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce rahotannin binciken farko sun bayyana wata alaka tsakanin 'yan sandan Najeriya da sojoji tare da 'yan bindiga da suka addabi al'umma.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya fallasa alakar da gwamnati ta gano tsakanin 'yan sanda, sojoji da 'yan bindigan Najeriya

Ya yi wannan jawabin ne yayin zantawa da tawagar yada labarai ta fadar shugaban kasa a gidan gwamnatin tarayya da ke Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

A yayin martani kan zargin cewa ko an samu wasu 'yan ta'adda da suka ratsa ta cikin tsarin tsaron kasar nan, El-Rufai ya ce:

"Eh, mun damu kuma ba za a ce abu ne da ba zai yuwu ba. Na kan yi jinkiri wurin amsa wannan tambayar. Binciken farko a kan masu daukar anuyin Boko Haram ya nuna alaka tsakanin wasu 'yan bindiga da jami'an 'yan sanda da na sojojin Najeriya. Suna da alaka sosai da 'yan bindigan."

Asali: Legit.ng

Online view pixel