An ba Amurka da Turai Goron Gayyata Su Shigo Harkokin Siyasar 2027
- Jam’iyyar NDC ta nemi Amurka da Tarayyar Turai su sa baki kan zargin kai hare-hare da tsoratar da ’yan adawa a Najeriya
- Jam’iyyar ta zargi gwamnatin APC da haifar da yanayin da ka iya hana jam’iyyun adawa samun damar shiga harkokin siyasar kasar
- Sai dai NDC ta ce ba za ta tsorata ko janye daga zaɓen 2027 ba, tana mai cewa dole ne a ƙirga tare da sanar da ƙuri’un da ta samu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Jam’iyyar NDC ta yi kira ga Amurka, Tarayyar Turai (EU) da sauran ƙasashen duniya da su sa baki kan zargin kai hare-hare, barazana da cin zarafin ’yan siyasa da magoya bayan jam’iyyun adawa gabanin zaɓen 2027.
Shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Cleopas Moses Zuwoghe, ne ya yi wannan kiran a ranar Laraba a Abuja, yayin wani taron manema labarai na ƙasa da ƙasa.

Source: Twitter
Vanguard ta wallafa cewa Zuwoghe ya bayyana damuwarsa kan abin da ya kira ƙaruwar hare-hare da tsoratar da ’yan adawa, tare da lalata kadarorin jam’iyyunsu a sassa daban-daban na ƙasar.
NDC ta zargi APC da danniya
Shugaban jam’iyyar ya zargi gwamnatin tarayya da jam’iyyar APC ke jagoranta da haifar da yanayin siyasa da ka iya korar jam’iyyun adawa daga harkokin siyasar Najeriya.
Ya buƙaci Amurka, Tarayyar Turai da sauran ƙasashen duniya su binciki rahotannin hare-haren, tare da matsa wa gwamnatin Najeriya lamba domin tabbatar da tsaro da gudanar da zaɓe cikin gaskiya da adalci.
Haka kuma, ya yi kira ga hukumomin tsaro su gudanar da bincike, su kama tare da gurfanar da waɗanda ake zargi da hannu a hare-haren.
Kiran NDC ga 'yan sanda
Rahoton Punch ya nuna cewa Zuwoghe ya ce kare rayuka da dukiyoyin jama’a babban nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnati.
Ya jaddada cewa hukumomin tsaro ya kamata su gudanar da aikinsu cikin ƙwarewa ba tare da nuna bambancin siyasa ba.
Ya kuma ce rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro na samun kuɗin gudanar da ayyukansu ne daga harajin ’yan Najeriya, don haka wajibi ne su kare kowa ba tare da la’akari da jam’iyyar da yake goyon baya ba.

Source: Facebook
Shugaban NDC ya nuna damuwa kan rashin kama ko hukunta waɗanda ake zargi da kai hare-hare kan ’yan adawa, yana mai gargaɗin cewa rashin ɗaukar mataki na iya ƙarfafa sake faruwar irin waɗannan laifuka.
Wike ya kara kaimu kan APC
A wani labarin, kun ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya nemi Shugaba Bola Tinubu da Sanata Abdulaziz Yari su ba shi damar gudanar da ayyukan yaƙin neman zaɓe a jihohin Imo da Kwara.
Wike ya bayyana cewa ya kammala aikin tattara magoya baya da shirya harkokin siyasa a Jihar Rivers da Babban Birnin Tarayya, inda aka ba shi alhakin gudanar da ayyukan.
Ministan ya yi wannan buƙata ne a wani taron tattaunawa da mazauna yankin da mambobin Rainbow Coalition a ƙaramar hukumar Gokana ta Jihar Rivers.
Asali: Legit.ng

