Gwamna Ya Tona Asiri, Ya Fadi Abin da Aka Rika Yaudarar Gwamnoni da Shi Suna Komawa APC

Gwamna Ya Tona Asiri, Ya Fadi Abin da Aka Rika Yaudarar Gwamnoni da Shi Suna Komawa APC

  • Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da amfani da Hukumar EFCC wajen tsoratar da gwamnonin adawa domin su koma APC
  • Makinde ya yi zargin cewa gwamnonin adawa na fuskantar barazanar bincike da yi musu baƙar magana idan suka ƙi sauya sheƙa zuwa APC
  • Ya kuma ce gwamnatin tarayya ta yi ƙoƙarin dora masa laifi da sunan kuɗin tallafin da aka bayar bayan fashewar bom a Bodija

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Oyo, Nigeria - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da amfani da Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) wajen tsoratar da gwamnonin adawa.

Gwamna Makinde ya yi ikirarin cewa gwamnatin Tinubu ta rika amfani da EFCC wajen matsala wa gwamnonjn adawa lamba tare da tilasta masu sauya sheka zuwa APC.

Kara karanta wannan

Da gaske shugaban INEC ya yi amfani da shafinsa na X wajen tallata Tinubu? Gaskiya ta bayyana

Gwamna Makinde.
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde yana jawabi a wurin kaddamar da ayyukan gwamnatinsa a Ibadan Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Makinde, dan takarar shugaban kasa na APM a zaben 2027, ya yi wannan zargi ne yayin wata hira da Arise News a ranar Juma’a.

Ya ce gwamnonin adawa da suka ƙi sauya sheƙa zuwa APC na iya fuskantar bincike da kuma yunƙurin shafa masu laifuffuka.

Ya fadi yadda aka yaudari gwamnoni

Ya yi gargaɗi cewa irin wannan mataki na iya kawo cikas ga tsarin dimokuraɗiyya mai jam’iyyu da dama a Najeriya.

"Abin da muka gani shi ne, wadannan gwamnoni su dawo APC. Idan ba haka ba, za a fra masu barazana," in ji Gwamna Makinde.

Domin bayyana abin da yake nufi, Makinde ya kawo misalin ɗan kwangila da ke gudanar da aiki a jihar da jam’iyyar adawa ke mulki, wanda zai iya fuskantar bincike kan kwangilolin gwamnati da mu’amalolin kuɗaɗensa.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

Ya ci gaba da cewa:

“EFCC za ta zo daga can. Ta ce, ‘Duba, nawa aka ba ka wannan kwangilar? Je ka kawo bayanan asusunka. Waɗanne mutane kake a kuɗi?’ Wannan ce halin da muke ciki a yau.”

Kara karanta wannan

Jigo a ADC ya gano abin da Tinubu ke fargaba kan zaben 2027

Zargin karkatar da kudin fashewar Bodija

Makinde ya kuma yi zargin cewa gwamnatin tarayya ta yi ƙoƙarin yi masa barazana kan kuɗin tallafin da aka bayar bayan fashewar bom a yankin Bodija, yana mai cewa gwamnatinsa ta riga ta biya mutanen da lamarin ya shafa diyya.

Ya ce gwamnatinsa ta haɗa kai da ƙungiyar injiniyoyi ta Najeriya da masu tantance darajar kadarori domin auna barnar da aka yi da kuma tantance kuɗin da ya kamata a biya waɗanda abin ya shafa.

Gwamnan ya ce:

"Kun san sun je wurin, sun tantance kadarorin, sannan muka biya waɗannan mutane kuɗinsu. Mun yi hakan ne tun kafin ma mu karɓi wani abu daga gwamnatin tarayya.”

Ya ƙara da cewa lokacin da aka tayar da batun, ya fitar da bayanan asusun jihar da ke nuna yadda aka gudanar da mu’amalar kuɗin.

Makinde ya fadi dalilin fitowa takara

Kun ji cewa gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana manyan dalilai hudu da suka sa ya yanke shawarar kalubalantar Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An fallasa shirin tafka magudi a babban zaben 2027

Makinde, ya ce matakin da ya dauka ba ya da nasaba da wata rashin jituwa ta kashin kai tsakaninsa da Tinubu ko kuma burinsa na zama shugaban kasa, sai dai damuwa ce kan makomar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262