Atiku Ya Sake Kifar da Tinubu, Ya Faɗi yadda Zai Dawo da Tallafi, Rage Farashin Fetur
- Atiku ya yi alkawarin rage farashin man fetur, dawo da tallafin mai da kuma ƙarfafa darajar Naira idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC ya bayyana cewa zai inganta rayuwar ’yan Najeriya ta hanyar bunƙasa masana’antun cikin gida
- Atiku ya yi wannan alƙawarin ne a lokacin gangamin ADC a Kogi, inda ya ce ba za a tilasta wa iyalai ci gaba da jure wahalar rayuwa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi alƙawarin dawo da tallafin man fetur, rage tsadar rayuwa da kuma ƙarfafa darajar Naira idan aka zaɓe shi shugaban Najeriya a zaɓen 2027.
Atiku, wanda yake takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin ADC ya kuma ce gwamnatinsa za ta ƙarfafa samar da kayayyaki a cikin gida domin rage dogaro da shigo da su daga ƙasashen waje.

Kara karanta wannan
Abin da muka sani kan batun APC ta rubuta wasika ga INEC don tabbatar da nasarar Tinubu

Source: Getty Images
Ɗan takarar ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin neman goyon baya da jam’iyyar ADC ta gudanar a jihar Kogi, kamar yadda daraktan yaɗa manufofinsa, Phrank Shaibu, ya bayyana a cikin wata sanarwa, cewar Punch.
Sanarwar ta bayyana cewa kamfen ɗin Atiku na neman sauƙaƙa rayuwa ya fi mayar da hankali kan iyalai da mutanen da suka kasa iya sayen abinci saboda tsadar kayayyaki da sufuri.
Atiku ya ce manufarsa ita ce taimaka wa iyalan da ke ƙoƙarin gudanar da rayuwa duk da ƙarancin kuɗaɗen shiga da hauhawar farashi.
Ya ce:
“Lokacin da muka ce za mu sake sauƙaƙa rayuwa, muna magana ne kan iyayen da ke ƙirga kuɗin da suka rage a jaka, da ma’aikatan da ke tunanin ko albashinsu zai iya kai su ƙarshen wata.
“Sun hallara nan da yawa ne saboda suna son a saurare su. Wahalar da suke ciki gaskiya ce, kuma fatansu ya cancanci samun amsa.”
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ƙara da cewa kamfen ɗinsa zai mayar da hankali kan rage farashin man fetur, taimaka wa ’yan Najeriya wajen samarwa da sayar da kayayyakinsu, tare da dawo da darajar kuɗin da suke samu.
Ya kuma ce al’ummar Kogi sun gaji da halin wahala ba tare da ganin lokacin da za a samu sauƙi ba, lamarin da ya sa suke ta kiran Shugaba Bola Tinubu ya sauka daga mulki.
Atiku ya bayyana cewa babu wani iyali da ya kamata ya roƙi damar rayuwa cikin mutunci a ƙasarsa, yana mai cewa bai kamata uwa ta zaɓi tsakanin ciyar da ’ya’yanta da biyan kuɗin makaranta ba.
Haka kuma, ya ce bai kamata ɗan kasuwa ya buɗe shagonsa da safe yana fargabar ko mutane za su iya sayen kayansa ba, ko matashi ya yi aiki tukuru amma ya kasa samun kuɗin komawa gida.
Ya gode wa al’ummar Kogi bisa tarbar da suka yi masa, sannan ya buƙaci magoya bayansa su ci gaba da gudanar da harkokinsu cikin lumana.
Ƙarin bayani na tafe.....
Asali: Legit.ng
