Shugaban APC Ya Ware Gwamnonin Arewa 7, Ya ba Su Shawara kan Goyon bayan Tinubu a 2027

Shugaban APC Ya Ware Gwamnonin Arewa 7, Ya ba Su Shawara kan Goyon bayan Tinubu a 2027

  • Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya buƙaci gwamnonin jam’iyyar a Arewa ta Tsakiya su haɗa kan masu ruwa da tsaki gabanin 2027
  • Yilwatda ya bayyana hakan ne a wajen gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC da aka gudanar a filin wasa na Azaria Road da ke Jos
  • Ya ce shugabannin siyasa a jihar Plateau sun haɗa kai dari bisa ɗari wajen marawa Tinubu baya domin tabbatar da nasarar APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Plateau, Nigeria - Shugaban APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda, ya buƙaci gwamnonin yankin Arewa ta Tsakiya su haɗa kan masu ruwa da tsaki a jihohinsu domin marawa Shugaba Bola Tinubu baya gabanin zaɓen 2027.

Yilwatda ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar da aka gudanar a filin wasa na Azaria Road da ke Jos, jihar Plateau.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kira ruwa, Dino Melaye ya yi masa tatas kan zaben 2027

Nentawe.
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda a wurin yakin neman zabe Hoto: Prof. Nentawe Yilwatda
Source: Facebook

The Cable ta ruwaito cewa Yilwatda ya bayyana gamsuwarsa da yawan mutanen da suka halarci gangamin, yana mai cewa hakan ya nuna yadda haɗin kan jam’iyyar ke ƙara ƙarfi da kuma jajircewarta wajen ganin Tinubu ya sake lashe zaɓe.

“Ƙarfinmu yana cikin haɗin kanmu, dabararmu ita ce tattara magoya baya, burinmu kuma shi ne samun nasara.
“Saboda haka, ina umartar dukkan gwamnoninmu, ’yan takarar gwamna da shugabannin APC a faɗin Arewa ta Tsakiya da su haɗa kan dukkan masu ruwa da tsaki a jihohinsu, su yi aiki tare domin samar da mafi yawan ƙuri’u ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
“Gangamin Jos ya nuna abin da za mu iya cimmawa idan muka tsaya tsayin daka kuma muka yi aikintare,” in ji shi.

Ya buƙaci al’ummar jihar Plateau su mayar da farin cikin da suka nuna a gangamin zuwa ƙuri’u, yana mai cewa dole ne jihar ta samar da gagarumar nasara ga shugaban ƙasa a zaɓe.

Kara karanta wannan

Tsaro ko tazarcen Tinubu: Matawalle ya bayyana babban burinsa a 2027

Shugaban APC ya ce a yanzu shugabannin siyasa a Plateau sun haɗa kai dari bisa ɗari wajen marawa Tinubu baya.

Ya ƙara da cewa sakamakon da za a samu a rumfunan zaɓe zai nuna goyon bayan al’ummar jihar Plateau ga shugaban ƙasa Tinubu.

APC na ganin Tinubu ya cika alkwari

Yilwatda ya bayyana Tinubu a matsayin mutumin da ke cika alƙawura, yana mai cewa shugaban ƙasar ya sauke nauyin alƙawuran da ya yi wa jihar.

Ya ce ayyukan da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun samar da kyakkyawan dalilin da zai sa jama’a su ƙara yarda da APC tare da ci gaba da mara mata baya.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin yakin neman zaben APC a Jos Hoto: Sunday Dare
Source: Facebook

Ya kuma buƙaci shugabannin jam’iyya, zaɓaɓɓun jami’ai, ’yan takara da masu wayar da kan jama’a da su ƙara ƙaimi wajen tattaunawa da masu zaɓe, domin tabbatar da cewa farin cikin da aka gani a Jos ya koma ƙuri’u masu yawa a faɗin yankin.

Alkawarin Tinubu kan zaben 2027

Kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ba za ta lamunci duk wani yunkurin haddasa tashin hankali ko tsoratar da masu kada kuri’a a zaben 2027.

Shugaban ya ce gwamnatin tarayya za ta tabbatar da samar da isasshen tsaro domin bai wa ’yan kasa damar amfani da hakkokinsu na kundin tsarin mulki ba tare da fargaba ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262