Abubuwa 6 da Ya Kamata a Sani dangane da Shari’ar Auren Gwamnan Kano
Kano - Uwar ‘ya ‘yan Abba Kabir Yusuf ta yi kararsa a kotu, tana mai neman alkali ya raba aurensu na tsawon shekara da shekaru.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
A shari'ar Musulunci, mace tana da damar tsinka igiyar aure a kotu ta khul'i ta hanyar biyan shi wani kudi domin ya iya rage zafi.
Zancen shari’ar kotun ta dauki hankali musamman da aka ji gwamnan Kano ya yi wasu kalamai da ke nuna ya saki mai dakinsa.

Source: Twitter
Shari'ar auren Abba Kabir da Zainab Kwankwaso
Legit Hausa Mun dauko manyan abubuwa dangane da wannan shari’a da ya kamata mutane su sani.
A ina aka shigar da karar?
Zainab Musa Kwankwaso ta kai karar ta mai lamba CV/97/26 ne a wata kotu da ake kira ‘Upper Area’ a birnin tarayya na Abuja.

Kara karanta wannan
Kano ta ɗauki zafi, Gwamna Abba ya yi kalaman da ake zargin ya nuna ya saki matarsa
A dokoki da tsarin mulkin kasa, irin wadannan kotuna suna karkashin kotunan shari’ar Musuluncin Najeriya da suke garin Abuja.
Daga wannan kotu ne sai kara ta tafi zuwa kotun daukaka kara na shari’ar Musulunci a Najeriya.
Wace ce ta kai kara a kotu?
Zainab Musa Kwankwaso wanda ta nemi a raba aurensu, kusan diya ce a wurin tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso.
Mahaifinta yaya ne ga ‘dan siyasar wanda a baya shi ne uban gidan Abba Kabir Yusuf a siyasa.
Kakanta shi ne Dagacin Kwankwaso wanda daga baya Ado Bayero ya nada shi a matsayin Majidadin Kano kuma Hakimin Madobi.
Ta bangaren uwa kuwa, kakar kakarta Aisha ta fito ne daga gidan Sarkin Kano, Abdullahi Maje Karofi, wato jikantar Sarki Ibrahim Dabo.
Hakan yana nufin sun hada kakanni da Alhaji Abba Kabir ta wajen Sarki Abdullahi Maje Karofi.
Alakar Zainab da Rabiu Kwankwaso
An ce Sanata Rabiu Kwankwaso ya aurar da ita ga Abba Kabir Yusuf lokacin yana ministan tsaro a gwamnatin Olusegun Obasanjo.
A wancan lokaci, Abba Kabir Yusuf hadimi ne wajen Kwankwaso wanda ya suka bar aikin gidan ruwa tare da shi tun shekarar 1992.
Alkalin da ke sauraron shari’ar
Mai shari’a Ado Mukhtar Ahmed Esq. da zai yi zama kan karar mutumin Kano ne wanda kuma ya yi karatunsa a gida a jami’ar nan ta Bayero.
A shekarar 2007 ya zama lauya kuma ya koma makarantarsa ya yi karatun digiri na biyu, kafin ya soma aikin alkali a Abuja tun shekarar 2011.
Daga shafin yanar gizon kotun Abuja, za a ga cewa an zabe sa a matsayin shugaban kungiyar alkalan birnun tarayya daga 2020 zuwa 2023.
Daga mataimakin darekta a 2022 na irin wadannan kotuna da ke Abuja ya zama darekta a halin yanzu.
Lauyan da ya shigar da kara
Aliyu Musa Baba shi ne lauyan da ya shigar da kara, yana mai wakiltar Zainab Musa Kwankwaso, tun 2024 yake aikin lauyan shari'ar Musulunci.
Legit Hausa ta samu labarin cewa lauyan ya yi karatun sakandarensa ne a makarantar FGC Kiyawa da kuma na digiri a jami’ar UNIMAID a Borno.
A shekarun bayan nan ya gama karatun lauya kuma ya samu horo har ya fara tsaya wa a Kotun koli, asalinsa mutumin Potsikum ne daga Yobe.

Source: Facebook
Wane ne yake kare Abba Kabir a kotu?
Zuwa yau 17 ga watan Nuwamba 2026, ba mu samu labarin lauyan da gwamna ya dauka domin ya ba shi kariya a shari’ar da ake yi a Abuja ba.
Abin da muka samu labari daga Daily Trust shi ne Sanusi Bature Dawakin Tofa ya wakilci Mai girma Abba Kabir a zaman da aka yi ranar Talata.
Yaushe gwamna da matarsa za su koma kotu?
Sanusi Bature Dawakin Tofa shi ne kakakin gwamnan Kano kuma kwanan nan ya zama Kwamishinan yada labarai da harkokin gida.
Kwamishinan ya nemi karin lokaci da kotu ta zauna, kuma lauyan mai kara bai yi adawa da hakan ba don haka alkali ya daga kara sai 15 ga Disamba.
Idan har auren ya kare, ba mamaki ba ne a ji lauyan da ya shigar da kara ya nemi kotu ta yi watsi da shari'ar kafin lokacin da za a sake yin zama.

Kara karanta wannan
Lamari ya yi tsanani har kotu tana yi wa ministan Tinubu barazana da dauri a kurkuku
Jita-jitar sasanta Gwamna Abba da matarsa
Da farko an fara jin rade-radin cewa an fara daukar mataki domin sasanta Mai girma gwamnan Kano da matarsa ta biyu, Zainab Musa Kwankwaso.
Har an ce Abdullahi Umar Ganduje zai jagoranci malamai da wasu manya zuwa gidan Rabiu Kwankwaso da nufin a dinke barakar da aka samu.
Amma bayanan da suka fito daga baya sun nuna da wahala a iya dawo da wannan aure a halin yanzu.
Asali: Legit.ng

