Babbar Magana: Matar Gwamna Abba na Jihar Kano Ta Nemi Saki a Kotu, Ta Fadi Dalili
- Zainab Musa Kwankwaso, matar Gwamna Abba Yusuf ta biyu, ta shigar da ƙarar neman kashe aurensu a wata kotun Shari’a da ke Abuja
- Takardar sammaci ta umarci gwamnan da ya gurfana a gaban kotun ranar 17 ga Nuwamba, 2026
- Zainab ta ce soyayya da kusancin da ke tsakaninsu sun lalace, inda ta bayyana shirinta na biyan Gwamna Abba sadakin da ya biya lokacin aurensu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Zainab Musa Kwankwaso, matar Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf ta biyu, ta shigar da ƙarar neman a kashe aurensu a Kotun Shari’a da ke Gudu, Abuja.
Takardar sammaci mai lambar CV/97/26 ta umarci gwamnan da ya bayyana a gaban kotun a ranar 17 ga Nuwamba, 2026.

Source: Facebook
Daily Nigerian ta ruwaito cewa Zainab, wadda ’yar Sanata Rabiu Kwankwaso ce, ta auri aAbba Kabir ne a ranar 29 ga Yuli, 2006, lokacin da take aiki a matsayin hadimar mahaifinta, sun haifi 'ya'ya shida.

Kara karanta wannan
2027: Gwamna ya ce nasarorin da ya samu za su taimaka masa wajen zama shugaban ƙasa
Majiyoyi sun ce sabanin da Gwamna Abba ya samu da ubangidansa kuma surukinsa watau Kwankwaso, ba iya harkar siyasa ya shafa ba, har da batun aurensa da Zainab.
Yadda Zainab ta bar gidan gwamnati
Rahotanni sun ce a ranar 28 ga Oktoba, matar gwamnan ta bar gidan gwamnatin Kano zuwa gidan mahaifinta da ke Miller Road, Kano, kafin daga bisani ta hau jirgin sama zuwa Abuja ba tare da rakiyar jami’in ’yan sanda da ke tsaronta ba.
’Dan sandan da ke yi mata rakiya, wanda ake zargin ya fahimci cewa akwai wani abu da ba daidai ba, ya sanar da manyansa da ke gidan gwamnatin Kano, waɗanda daga bisani suka sanar da gwamnan.
Majiyoyi sun ce da farko an umurci jami’an tsaron filin jirgin sama da kada su bari ta hau jirgin.
Sai dai daga baya aka ba ta damar tafiya bayan jami’an sun nuna damuwar cewa hana ta shiga jirgin na iya haifar da hayaniya a filin jirgin.
Rahoton Daily Nigerian ya nuna an kama jami’an tsaron da aka ɗora wa aikin gadin ɗakinta a gidan gwamnatin Kano, da kuma wasu jami’an tsaron da ke aiki a gidan Kwankwaso, daga bisani aka sake su bayan sun amsa tambayoyi.
An ce ce ’yar’uwar Zainab da babban ɗan’uwanta, Ado Kwankwaso, an gayyace su zuwa ofishin ’yan sanda domin amsa tambayoyi kan zargin taimaka mata ta bar Kano.
Dalilin neman kashe auren
A cikin bayanan ƙarar da ta shigar a kotu, Zainab ta bayyana cewa aurenta da Abba ya samu matsala, inda ta ce an daɗe ana fama da rashin kulawa, soyayya, ƙauna da kusancin zuciya tsakanin ma’auratan.
Ta shaida wa kotun cewa ita ma ta rasa soyayya da ƙaunar da take yi wa gwamnan, sannan ta fara jin tsananin ƙyamar ci gaba da auren.

Source: Facebook
Ta kuma bayyana fargabar cewa ci gaba da zama a cikin auren zai iya hana ta kiyaye iyakokin da Allah ya tsara kan wajibcin da ke kan mace ga mijinta.
Bisa ga takardun kotun, Zainab ta ce duk ƙoƙarin da aka yi na sasanta su da dawo da zaman lafiya a tsakaninsu ya ci tura. Ta ƙara da cewa zuciyar gwamnan ta juya gaba ɗaya daga auren.
Zainab na neman a raba aurensu ta hanyar khul’i, wadda hanya ce a shari’ar Musulunci da mace za ta iya bi domin neman rabuwa da mijinta, yawanci ta hanyar biyan diyya ko mayar da sadakin da ta karɓa.
Gwamna Abba ya kare Tinubu
Kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabur Yusuf ya ce nan ba da daɗewa ba ’yan Najeriya za su fara amfana da sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakai masu wuya amma sun zama wajibi domin daidaita tattalin arzikin ƙasar da kuma sanya ta a turbar ci gaba.
Asali: Legit.ng

