"Yadda Pater Obi da Kwankwaso Za Su Kifar da Tinubu a Zaben 2027 da Taimakon Allah"

"Yadda Pater Obi da Kwankwaso Za Su Kifar da Tinubu a Zaben 2027 da Taimakon Allah"

  • Babachir Lawal ya ce Peter Obi da mataimakinsa, Rabiu Musa Kwankwaso, na samun goyon bayan Ubangiji domin kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027
  • Tsohon sakataren gwamnatin tarayya ya ce dimbin goyon bayan da ’yan takarar ke samu daga jama’a alama ce ta falalar Ubangiji a kansu
  • Lawal ya ce NDC na da kwarin gwiwar kayar da jam’iyyar APC mai mulki, yana mai cewa sun riga sun samar da tsare-tsare da dabarun cimma wannan buri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Babachir Lawal ya ce Allah na tare da Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC da mataimakinsa, Rabiu Musa Kwankwaso, domin su kayar da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Jigon na NDC ya ce dimbin goyon bayan da Obi da Kwankwaso ke samu daga jama’a na nuna cewa suna samun falala da taimako daga Allah.

Kara karanta wannan

Abin da na jikin Tinubu suka gano wanda ya nuna Arewa na tare da shugaban ƙasa

Babachir Lawal.
Tsohon sakataren Gwamnatin tarayya, Babachir Lawal Hoto: Babachir David Lawal
Source: Twitter

Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise TV, inda

“Na sha gaya wa duk wanda ya tattauna da ni cewa Peter Obi da Rabiu Kwankwaso suna tare da falalar Ubangiji a rayuwarsu, wadda ke sa mutane su so su.

“Jama’a na son su. Kawai su je kasuwa ku ga ikon Allah, ba sai sun ɗauki mutane haya domin su halarci gangaminsu ba, mutane kan fito da kuɗinsu domin halartar tarukan," in ji shi.

Ya ce gogewarsa a harkokin siyasa ta ba shi damar gane alamomin da ka iya amfani ga ƙawancen ’yan adawa, yana mai cewa ya taɓa kasancewa a irin wannan matsayi a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari.

Babachir Lawal ya ce:

“Ba wannan ne karon farko da na tsinci kaina a irin wannan matsayi a siyasa ba. Na taɓa kasancewa haka a zamanin Buhari. Har da wannan shugaban ƙasarku, na taimaka masa har zuwa zaɓen fitar da gwani.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kwankwaso ya fito ya gayawa duniya wani halin Peter Obi

“Saboda haka, ni gogagge ne kuma na ƙware a wannan fanni. Ina iya ganin alamomi, kuma mun san wuraren da ake da gibi. Muna kuma aiki a kan waɗannan gibin.”

NDC na da kwarin gwiwar nasara

Lawal ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa NDC za ta kayar da APC mai mulki, yana mai cewa jam’iyyar ta riga ta samar da tsare-tsare da tsarin da za su taimaka mata cimma burinta.

Obi da Kwankwaso.
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi da mataimakinsa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Lawal ya yi watsi da damuwar da ake nunawa kan ficewar Yunusa Tanko, tsohon mai kula da tafiyar Obidient Movement a ƙasa, Nana Kazaure, Doyin Okupe da tsohon mataimakin sakataren yaɗa labarai na ƙasa na NDC daga sansanin Obi.

Ya ce ’yan siyasa na da ’yancin barin jam’iyyun da suke ciki idan ba su samu abin da suke tsammani ba.

NDC ta hango nasarar Peter Obi

Kun ji cewa jam’iyyar NDC ta bayyana kwarin gwiwar cewa dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi, zai iya samun gagarumar nasara a zaben 2027.

Ta ce hadin gwiwar magoya bayan Obi da tafiyar Kwankwasiyya na iya samar da karfin siyasa da zai kalubalanci APC a Arewa da Kudancin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262