Wanda NDC ta ba takarar gwamna ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a Bauchi

Wanda NDC ta ba takarar gwamna ya sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a Bauchi

  • Tsohon dan takarar gwamnan Bauchi a jam'iyyar NDC, Ibrahim Muhammad Kashim, ya shiga jam'iyyar APC mai-ci
  • Ya ce ya dauki matakin ne domin samun damar taka rawa wajen ci gaban jihar a karkashin jam'iyya mai mulki a tarayya
  • Ibrahim Muhammad Kashim ya ce sauya shekarsa ba ta da alaka da neman mukami ko wani abin don karon kansa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Bauchi - Ibrahim Muhammad Kashim wanda a da shi aka yi tunanin zai yi wa NDC takarar gwamna a jihar Bauchi a 2027 ya sauya-sheka.

Ibrahim Muhammad Kashim ya bayyana sauya shekarsa ne a wani taron da aka gudanar a sakatariyar APC da ke garin Bauchi ranar Litinin.

Daily Trust ta rahoto ya ce ya koma APC ne saboda jam'iyyar tana da damar taimaka wa Bauchi wajen samun ci gaba da kuma farin jinin da ta yi.

Kara karanta wannan

Alkawarin da Atiku Abubakar ya yi wa mutane da ADC ta je kamfen ADC a Bauchi

‘Dan siyasar yana ganin cewa Bauchi za ta fi amfana da ayyukan gwamnatin tarayya a jam’iyyar APC.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi ya ce APC ce jam'iyya mai mulki a matakin tarayya, kuma tana da karfi da tasiri a fadin Arewacin Najeriya.

Ibrahim Kashim ya ce ba za a iya yin wasa da makomar jihar Bauchi ba ta hanyar kasancewa a jam'iyyar da ba ta da isasshen tasiri a matakin kasa ba.

Kashim ya kara da cewa ba saboda neman mukami ko wata matsala ta kansa ba ne ya canza sheka, illa wani zabi da ya yi bayan nazari kan makomar jihar.

Duk da ya yi murabus daga jam'iyyar NDC a ranar 16 ga Oktoba, 2026, amma ya jaddada cewa har yanzu yana da burin ganin Bauchi ta samu ci gaba.

Business Day ta rahoto shi yana cewa har gobe yana nan a kan bakarsa na ganin ya goyi bayan wanda zai kawo wa matasa da mata cigaba a Bauchi.

Ya ce manyan abubuwan da yake son ganin an inganta sun hada da samar da ayyukan yi ga matasa, karfafa mata, bunkasa noma, inganta ilimi da kiwon lafiya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya leƙo babbar matsalar ƴan Plateau, ya ɗauka masu alƙawari

A karshe, ya yi kira ga magoya bayansa da sauran abokan siyasa da su mara masa baya wajen komawa APC domin haka kai wajen neman kowa cigaba.

Kashim yana ganin maslaha idan Bauchi ta bi layin jam’iyyar APC mai iko da Gwamnatin tarayya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng