Wata Sabuwa: 'Yan Kwankwasiyya da Gwamnatin Abba Sun Kaure da Cacar Baki
- Gwamnatin Kano ta musanta zargin cewa wasu ’yan daba sun kai hari kan ayarin motocin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a karamar hukumar Bichi
- Sai dai kungiyar Kwankwasiyya ta dage cewa an kai harin, tare da zargin gwamnatin jihar da kokarin wanke kanta daga lamarin
- Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi, ya yi Allah wadai da harin, yana mai cewa an jikkata mutane tare da lalata motoci kusan bakwai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Kano – Gwamnatin jihar Kano da kungiyar Kwankwasiyya sun yi musayar yawu kan zargin kai hari ga ayarin motocin mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a karshen makon da ya gabata.
Dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar NDC, Aminu Gwarzo, ne ya fara zargin cewa wasu ’yan daba da gwamnatin jihar ta turo ne suka kai wa ayarin motocin Kwankwaso hari yayin ziyarar yakin neman zabe a karamar hukumar Bichi ranar Lahadi.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa lamarin ya janyo martani daga gwamnatin jihar da kuma kungiyar Kwankwasiyya, inda kowannensu ya zargi daya bangaren da rashin gaskiya.
Gwamnatin Kano ta musanta kai harin
Kwamishinan Yada Labarai na jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya yi watsi da zargin cewa an kai hari kan ayarin motocin Kwankwaso a Bichi, yana mai bayyana rahoton a matsayin kirkirarren labari.
Dawakin Tofa ya zargi kungiyar Kwankwasiyya da kitsa labarin domin neman tausayin jama’a, inda ya ce ba a gabatar da hotuna ko bidiyon da ke tabbatar da faruwar lamarin ba.
Kwankwasiyya ta mayar da martani
A martaninta, kungiyar Kwankwasiyya ta ce jihar Kano mallakin dukkan mazaunanta ce, ba wai mutanen da ke rike da mukaman gwamnati kadai ba.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Dakta Habibu Mohammed, ya fitar, ta ce gwamnati na da alhakin kare lafiyar dukkan al’ummar jihar ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ba.

Kara karanta wannan
"Ku kasance cikin shiri": Abin da Kwankwaso ya gayawa magoya baya bayan kai masa hari
Kungiyar ta soki kwamishinan yada labarai bisa bukatar ganin hotuna da bidiyo maimakon barin jami’an tsaro su gudanar da bincike kan zargin harin.
Ta kuma ce aikin tabbatar da gaskiyar abin da ya faru da kuma gano wadanda suka aikata laifi ya rataya ne a wuyan hukumomin tsaro, ba wadanda abin ya shafa ba.

Source: Twitter
Kwankwasiyya ta bukaci rundunar ’yan sandan jihar Kano ta gudanar da bincike kan lamarin, ta gano wadanda suka kai harin tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu.
Haka kuma, Punch ta rahoto cewa ta bukaci a binciki rahotannin lalata motoci da jikkata wasu daga cikin mutanen da ke tare da Kwankwaso.
Kungiyar ta yi kira ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya tabbatar da tsaron dukkan ’yan siyasa da magoya bayansu a jihar, tana mai gargadin cewa bai kamata a mayar da hamayya ta siyasa zuwa tashin hankali ba.
Maganar da Obi ya yi
A wani labarin, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya yi Allah wadai da harin da aka kai wa ayarin motocin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
A bayanin da ya yi, Obi ya bayyana cewa mutane da dama sun jikkata a harin, yayin da aka lalata motoci kusan bakwai da ke cikin ayarin.
Ya bukaci rundunar ’yan sanda da sauran hukumomin tsaro su gudanar da bincike cikin gaggawa, tare da kama wadanda suka kai harin da kuma wadanda suka dauki nauyinsa.
Asali: Legit.ng

