'Na Samu Tabbaci': Tinubu Ya Ce Zai Je Ya Yi Bacci bayan Abin da Ya Gani a Kebbi

'Na Samu Tabbaci': Tinubu Ya Ce Zai Je Ya Yi Bacci bayan Abin da Ya Gani a Kebbi

  • Shugaba Bola Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar samun kuri'un al'ummar Jihar Kebbi a zaben shugaban kasa na 2027, yana neman wa'adin mulki na biyu
  • Tinubu ya bayyana hakan ne yayin gangamin yakin neman zabensa na APC a Birnin Kebbi, inda ya nemi jama'a su sake zabensa domin kammala ayyukansa
  • Gwamna Nasir Idris da Sanata Abdulaziz Yari sun tabbatar wa Tinubu da cikakken goyon bayan Kebbi da sauran jihohin Arewa maso Yamma a zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kebbi - Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa zai samu goyon bayan al'ummar Jihar Kebbi a zaben shugaban kasa na 2027.

Tinubu ya ce zai iya komawa gida ya kwanta barci cikin kwanciyar hankali, saboda ya san al'ummar jihar za su fito su zabi jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

"Alamu da lissafin siyasa sun nuna wanda zai lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027"

Tinubu ya godewa yan jihar Kebbi
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

Rokon Tinubu ga yan Najeriya

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na APC da aka gudanar a Birnin Kebbi, cewar PM News

Ya bukaci 'yan Najeriya su sake ba shi damar mulki a karo na biyu, domin ya kammala shirye-shirye da ayyukan da gwamnatinsa ta fara.

Da yake jawabi ga mahalarta taron, Tinubu ya ce:

"Zan iya komawa gida cikin kwanciyar hankali in yi barci. Na san za ku fito ku kada kuri'a, daga sama har kasa, APC SAK."

Tinubu Ya Ce Allah Ne Ke Ba Da Mulki

Shugaban kasar ya kuma yi amfani da damar wajen tunatar da al'umma cewa Allah ne ke ba da mulki ga wanda Ya so, cewar Punch.

Ya ce Allah ne ya ba shi damar zama shugaban kasa a zaben 2023, kuma yanzu ya dawo neman goyon bayan 'yan Najeriya domin wa'adin mulki na biyu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya leƙo babbar matsalar ƴan Plateau, ya ɗauka masu alƙawari

A cewarsa:

"Allah ne kadai ke ba da mulki ga wanda Ya so. Na nemi mulkin, Ya ba ni wannan girmamawa, dama da mukami a karo na farko.
"A wannan karon, na zo gabanku ne domin neman goyon bayanku na wa'adin mulki na biyu, don kammala abin da na fara. Lokacinku zai zo a gaba."
Tinubu ya yi alkawari ga yan Kebbi
Dandazon al'umma yayin kamfen APC a Kebbi da Bola Tinubu. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

Gwamnan Kebbi ya dauki alkawari

A yayin taron, Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya tabbatar wa shugaban kasa cewa jihar za ta ba jam'iyyar APC dukkan kuri'unta.

Gwamnan ya bayyana cewa Kebbi na tare da APC da Bola Ahmed Tinubu da kuma mataimakinsa, Kashim Shettima.

Ya ce:

"Kebbi jiha ce ta APC, kuma Kebbi na tare da Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima. Ina tabbatar muku cewa Kebbi za ta ba APC kashi 100 na kuri'unta."

Haka kuma, gwamnan ya yi amfani da damar wajen rokon Tinubu ya taimaka wajen fara gudanar da ayyukan tashar jiragen ruwa ta cikin gida ta Tsamiya da ke karamar hukumar Bagudu.

Kara karanta wannan

Shawara mai kama hankali da Sheikh Gumi ya ba ƴan siyasa a Najeriya

Alkawarin Tinubu ga yan Plateau

A wani labarin, an ji cewa shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shiryen girka kyamarorin sa ido a Plateau.

Gwamnatin tarayya ta dauki jami'an tsaron gandun daji 1,000 aiki, inda a halin yanzu suke karbar horon da zai ba su damar fara gudanar da ayyukansu.

Gwamna Caleb Mutfwang ya bayyana shirin samar da guraben ayyukan yi ga matasa 2,000 ta hanyar hada su da kamfanoni da kungiyoyin kasashen waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.