Jigo a ADC Ya Gano Abin da Tinubu Ke Fargaba kan Zaben 2027

Jigo a ADC Ya Gano Abin da Tinubu Ke Fargaba kan Zaben 2027

  • Solomon Dalung ya yi zargin cewa Tinubu na tsoron zaɓen 2027, duk da cewa ya shafe shekaru huɗu a kan mulki
  • Dalung ya ce ko da an zaɓi mutum daga kan titi ya fafata da Tinubu, zai iya kayar da shugaban ƙasar
  • Jigon ADC ya zargi APC da hana jam’iyyun adawa gudanar da tarukan kamfen ta hanyar rufe wuraren taro da ofisoshin jam’iyyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Solomon Dalung, ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sha kaye a zaɓen 2027.

Dalung ya yi zargin cewa shugaban ƙasar na tsoron fuskantar masu zaɓe, duk da cewa ya shafe shekaru huɗu a kan mulki.

Dalung ya ce Tinubu na fargabar 2027
Solomon Dalung da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: Comrade Solomon Dalung, Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Channels Television a shirin Politics Today ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamban 2026.

Kara karanta wannan

Jigo a ADC ya ce an samu kiran waya daga kabarin Buhari kan wanda za a zaba a 2027

Dalung ya ce Tinubu zai sha kaye

Dalung ya yi wannan hasashen ne yayin da ake tambayarsa yadda jam’iyyun adawa za su iya tinkarar ƙarfin APC, musamman albarkatun da take da su, a daidai lokacin da ADC ke fama da rikicin shugabanci da ƙalubalen shari’a.

Duk da haka, ya jaddada cewa jam’iyyar ADC a shirye take ta fafata da Tinubu a zaɓe.

“Tun lokacin da na fara siyasa, kamar yadda na saba faɗa, an shigar da ni harkar siyasa tun ina ƙarami. Ban taɓa ganin shugaban ƙasa mai rauni a lokacin zaɓe kamar Bola Ahmed Tinubu ba.
“Ko da ka ɗauko wani mutum daga kan titi ka sanya sunansa a takardar zaɓe domin ya fafata da Tinubu, zai kayar da shi.” In ji shi.

Me Tinubu ya ke fargaba kan 2027?

Jigon ADC ɗin ya kuma yi zargin cewa Tinubu na fargabar zaɓen da ke tafe, duk da kasancewarsa shugaban ƙasa na tsawon shekaru huɗu.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An fallasa shirin tafka magudi a babban zaben 2027

Ya ƙalubalanci shugaban ƙasar da APC su bar sakamakon zaɓe ya kasance hannun masu kaɗa ƙuri’a.

"Bola Tinubu yana tsoron zaɓe matuƙa, duk da cewa ya shafe shekaru huɗu a kan mulki. Duk abin da muke gani a ADC, muna cewa mu haɗu a wajen zaɓe.
“Kun ce ƙuri’a ce ta kai ku kan mulki, to ku zo mu haɗu a wajen zaɓe.” In ji shi.

Dalung ya yi zargi kan jam'iyyar APC

Dalung ya kuma zargi APC da kawo cikas ga ayyukan kamfen na jam’iyyun adawa, inda ya yi ikirarin cewa ana rufe wuraren taruka, ƙwace otal-otal da kuma kulle ofisoshin jam’iyyun siyasa.

Ya kwatanta halin da ake ciki da lokacin zaɓen 2014, inda ya ce da a ce PDP ta ɗauki irin waɗannan matakai a lokacin, da APC ba ta samu wuraren gudanar da kamfen ba sai kan tituna.

“Babu wanda za a ɗora wa laifi sai Tinubu. Me ya sa? Domin a tarihin Najeriya, mun ga jam’iyyun adawa suna fafatawa a zaɓe, amma ba mu taɓa ganin irin wannan yanayi ba.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar Amaechi ya bar gwamnatin Atiku idan suka hau mulki

“Da a ce PDP ta rika rufe wuraren tarukan kamfen, ƙwace otal-otal da kulle ofisoshin jam’iyyu a shekarar 2014, da APC ba ta da wurin gudanar da kamfen sai kan tituna.” In ji shi.
Dalung ya yi magana kan Tinubu
Tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung Hoto: Comrade Solomon Dalung
Source: Getty Images

Maganar Dalung kan ziyarar Aisha wajen Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa Solomon Dalung, ya yi magana kan ziyarar da tsohuwar uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari, ta kai wa Alhaji Atiku Abubakar.

Solomon Dalung ya yi zargin cewa tsohuwar uwargidan shugaban ƙasa, Aisha Buhari, ta ziyarci Atiku Abubakar domin sanar da shi cewa an miƙa masa kuri’u miliyan 12 na marigayi Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng