Yan Takarar Gwamnan ADC Sun Dauki Zafi kan Hukuncin Hana Atiku Takara a Zaben 2027
- Ƙungiyar ’yan takarar gwamnan ADC ta ce hukuncin da ya soke shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin David Mark barazana ne ga ’yancin dimokuraɗiyya
- Sun buƙaci kotunan ɗaukaka ƙara su gaggauta nazarin hukuncin, tare da kira ga Tinubu da APC su mutunta tsarin jam’iyyu da dama
- ’Yan takarar sun nemi AU, ECOWAS, Majalisar Ɗinkin Duniya da sauran ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa su sa ido kan yadda ake wa ’yan adawa a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ƙungiyar ’yan takarar gwamnan jihohi na ADC a Najeriya ta soki hukuncin Mai Shari’a Peter Lifu, wanda ya soke Kwamitin Ayyuka na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark.
Ƙungiyar ta bayyana hukuncin a matsayin “babban hari kan ’yancin dimokuraɗiyya, kuma matakin da zai iya haddasa hargitsi a zaɓen 2027.”

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa a hukuncinsa, Mai Shari’a Lifu ya soke shugabancin David Mark tare da dukkan ayyukan da aka gudanar ƙarƙashin wannan shugabanci.
Daga cikin ayyukan da wannan hukunci ya rusa har da zaɓen ’yan takarar jam’iyyar ADC na zaɓen 2027, wanda ya kunshi ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar.
Yan takarar gwamnan ADC sun yi martani
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis, Zakari Mohammed, ɗan takarar gwamnan ADC a Jihar Kwara, tare da wasu ’yan takarar, ya yi kira ga ƙasashen duniya da ƙungiyoyin dimokuraɗiyya da su shiga tsakani.
Ya ambaci Tarayyar Afirka (AU), Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), Commonwealth da sauran cibiyoyin dimokuraɗiyya.
A cewarsa, ya kamata su ɗauki mataki kan abin da suka kira “barazanar da ke ƙara fuskantar siyasar ’yan adawa a Najeriya.”

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Dalung ya hango matsalar da za ta iya zama hatsari ga ADC a zaben 2027
Mohammed ya ce sun ga ya zama dole su yi magana kan hukuncin da Mai Shari’a Lifu ya yanke a ranar 5 ga Nuwamba, saboda tasirinsa ya wuce batun cikin gida na jam’iyyar ADC.
“Wannan hukunci ya haifar da muhimman tambayoyi game da daidaito wajen yanke hukuncin shari’a, shiga harkokin siyasa, ’yancin cibiyoyin dimokuraɗiyya da kuma makomar dimokuraɗiyya mai tsarin jam’iyyu da dama a Najeriya,” in ji shi.
Ƙungiyar ta ce halin da ake ciki ya tilasta mata yin kira ga kotunan ɗaukaka ƙara da su gaggauta nazarin hukuncin Mai Shari’a Lifu, domin su yanke hukunci kan batutuwan da aka gabatar bisa tanade-tanaden kundin tsarin mulki.
Sun aika sako ga Tinubu da APC
’Yan takarar sun kuma buƙaci bangaren zartarwa na gwamnati da sauran ’yan siyasa da su guji duk wani mataki da zai iya tsoratarwa, yin tasiri ko kawo cikas ga ’yancin bangaren shari’a.

Source: Twitter
Sun yi kira kai tsaye ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shugabannin APC da su fito fili su sake1 tabbatar da goyon bayansu ga tsarin dimokuraɗiyya mai bai wa jam’iyyu da dama damar fafatawa.
Sun buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ci gaba da kasancewa mai zaman kanta da rashin nuna bambanci, tare da bin kundin tsarin mulki da dokokin zaɓe da suka dace.

Kara karanta wannan
Tinubu ya kwantar da hankulan 'yan Najeriya, ya fadi shirinsa kan kawo karshen rashin tsaro
Atiku zai shiga zaben 2027
Kun ji cewa jam’iyyar adawa ta ADC ta tabbatar da cewa za ta shiga zaɓen 2027 duk da rikicin shugabanci da ƙalubalen shari’a da take fuskanta.
Mai magana da yawun jam’iyyar ADC na ƙasa, Bolaji Abdullahi, ya ce tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, zai kasance cikin ’yan takarar 2027.
Asali: Legit.ng
