Kwamishina Ya Kare Alkawarin Samar da Kuri'u Miliyan 2 ga Tinubu a 2027
- Kassim Afegbua ya ce burin samun ƙuri’u miliyan 2.5 ga Tinubu a Edo abu ne mai yiwuwa, bisa yawan masu rajistar zaɓe a jihar
- INEC ta ƙiyasta yawan masu rajistar zaɓe a Edo zuwa miliyan 2.865, kamar yadda kwamishinan ya bayyana
- Gwamna Monday Okpebholo zai zagaya kananan rumfunan zaɓe 192 domin neman goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Edo - Kwamishinan Yaɗa Labarai da Dabarun Sadarwa na Jihar Edo, Hon. Kassim Afegbua, ya kare alƙawarin Gwamna Monday Okpebholo na samar wa Shugaba Bola Tinubu ƙuri’u miliyan 2.5 a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Afegbua ya bayyana cewa wannan adadi ba wani buri ne da ya wuce ƙima ba, domin gwamnati na ganin za ta iya cimma shi idan aka yi la’akari da yawan masu rajistar zaɓe a jihar.

Kara karanta wannan
An hango abin da zai faru idan aka yi wa 'yan Najeriya karfa karfa kan Tinubu a 2027

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a safiyar ranar Lahadi, 15 ga watan Nuwamban 2026 a tashar Arise TV.
Adadin masu zaɓe a Edo
Kwamishinan ya ce Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa jihar Edo na da masu rajistar zaɓe miliyan 2.865.
A cewarsa, wannan adadi ne ya sa gwamnatin jihar ta sanya wa kanta burin samo wa Tinubu ƙuri’u miliyan 2.5 a zaɓen 2027.
“Yanayin da muka yi wannan magana a cikinsa shi ne, mun sanya wa kanmu wani buri. Bayan haka, yawan masu rajistar zaɓe, kamar yadda INEC ta fitar a makon da ya gabata, ya kai mutum miliyan 2.865. Me zai faru idan muka samu miliyan 2.5? Laifi ne?” In ji shi.
Afegbua ya ce gwamnatin jihar na gudanar da ayyukan raya ƙasa da suka haɗa da gina ababen more rayuwa, inganta ilimi da kiwon lafiya, da kuma bunƙasa harkokin jin daɗin al’umma.
Ya ƙara da cewa waɗannan ayyuka na daga cikin dalilan da gwamnati ke ganin za su sa mazauna jihar su amince da sake zaɓen Tinubu.
Dalilin neman sake zaɓen Tinubu
Kwamishinan ya ce alhakin gwamnatin jihar shi ne ta shawo kan masu zaɓe su mara wa Tinubu baya domin ya sake yin wa’adi na biyu.
Ya danganta hakan da ƙarin kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ke bai wa jihohi, yana mai cewa hakan na taimaka wa gwamnatocin jihohi wajen gudanar da ayyukan ci gaba.
A kalamansa:
“Alhakinmu shi ne mu lallashe su, mu roƙe su, mu yi kira gare su da su ba mutumin da ke samar da kuɗaɗen gudanar da ayyuka ta hanyar ƙara rabon kuɗaɗe ga jihohi damar ci gaba da mulki, domin su samu damar ganin ƙarin ci gaba.”
Afegbua ya kuma yi nuni da cewa ci gaba da mulki yana da muhimmanci wajen bunƙasa tattalin arziki.
Ya yi gargaɗin cewa sauya shugabanci akai-akai na iya kawo cikas ga aiwatar da manufofin gwamnati, musamman a lokacin da ake ganin tattalin arziki na fara daidaituwa.
Okpebholo zai zagaya mazabu 192
Kwamishinan ya bayyana cewa Gwamna Okpebholo na shirin zagaya dukkan mazabu 192 na jihar domin neman goyon bayan Tinubu.
Ya ce gwamnati za ta yi aiki tukuru wajen ganin an wayar da kan masu zaɓe, an ƙarfafa su su fito, sannan kuma an tabbatar an ƙirga ƙuri’unsu.
Afegbua ya jaddada cewa mutanen Edo a shirye suke su mara wa Tinubu baya a zaɓen 2027.
“Mutanen Edo a shirye suke. Za mu tabbatar da cewa Jihar Edo ta ba Shugaba Tinubu ƙuri’u, kuma muna alfahari da hakan. Za mu yi aiki tukuru domin cimma wannan buri.” In ji shi.

Source: Facebook
An yi gargadi kan kakaba Tinubu ga 'yan Najeriya
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin kakakin yaɗa labarai na jam’iyyar APC na ƙasa, Timi Frank, ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na tilasta wa Shugaba Bola Tinubu komawa kan mulki a zaɓen 2027 na iya jefa Najeriya cikin rikici.
Timi Frank ya ce ’yan Najeriya ba za su amince da sakamakon zaɓen da ya saɓa wa zaɓin da suka yi ta hanyar ƙuri’unsu ba.
Asali: Legit.ng

