Ana Batun Matsalar Aurensa, Gwamna Abba Ya Samu Babban Tagomashi kan Zaben 2027

Ana Batun Matsalar Aurensa, Gwamna Abba Ya Samu Babban Tagomashi kan Zaben 2027

  • Shugabannin ƙwadago da ’yan fansho sun ayyana goyon bayansu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ya sake neman kujerar gwamnan Kano a zaɓen 2027
  • Gwamnatin Kano ta sake ware Naira biliyan 5 domin biyan haƙƙoƙin tsofaffin ma’aikata, wanda ya kai jimillar kuɗin da ta ware Naira biliyan 37
  • Gwamnatin jihar ta sanya wa kanta burin kammala biyan bashin haƙƙoƙin fansho da alawus-alawus kafin watan Afrilun 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago da ’yan fansho a Najeriya sun bayyana goyon bayansu ga Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, domin ya sake tsayawa takara a zaɓen gwamna na shekarar 2027.

Sun bayyana matsayarsu ne yayin rabon kashi na bakwai na Naira biliyan 5 da gwamnatin jihar ta ware domin biyan bashin alawus-alawus na ritaya da haƙƙoƙin iyalan ma’aikatan da suka rasu.

Kara karanta wannan

Masu bukata na musamman sun kafa sharadi ga Gwamna Abba kan samun tazarce a 2027

Gwamna Abba ya samu tagomashi
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Isah Muhammad Salisu
Source: Facebook

An gudanar da taron ne a fadar gwamnatin jihar Kano, inda aka kuma yaba wa gwamnatin Yusuf kan ƙoƙarin da take yi na biyan kuɗaɗen da ake bin tsoffin ma’aikatan gwamnati.

An mara wa Gwamna Abba baya

Daga cikin waɗanda suka bayyana goyon bayansu ga gwamnan akwai tsohon shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Kwamared Ayuba Wabba.

Sauran sun haɗa da mataimakin shugaban NLC na ƙasa, Kwamared Kano Ado Minjibir; shugaban Ƙungiyar ’Yan Fansho ta Najeriya, Kwamared Mazi Goodwin Abumisi; da shugaban NLC na jihar Kano, Kwamared Kabiru Inuwa.

Shugabannin ƙwadagon da wakilan ’yan fansho sun yaba wa gwamnatin Abba kan yadda take ci gaba da ƙoƙarin rage bashin kuɗaɗen fansho da alawus-alawus da ake bin tsoffin ma’aikata.

Sun kuma yaba musamman kan fitar da sabon kashi na Naira biliyan 5, wanda ya kai jimillar kuɗin da gwamnatin jihar ta ware domin biyan waɗannan basussuka zuwa Naira biliyan 37.

Kara karanta wannan

Sabon tsarin da Kwankwaso yake so a yi amfani da shi a zaben shugaban kasa a Najeriya

Sun bukaci a sake zaɓen gwamnan a 2027

A jawabansu daban-daban, shugabannin sun bayyana amincewarsu da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, tare da kira ga al’ummar Kano da su sake zaɓensa a 2027.

Sun ce hakan zai ba shi damar ci gaba da ayyukan da suka ce ana yi domin inganta walwalar ma’aikata da ’yan fansho a jihar.

Wannan goyon baya ya zo ne a daidai lokacin da gwamnatin Kano ke ƙara ƙaimi wajen biyan bashin fansho da ta gada daga gwamnatocin baya.

Gwamnati na son kammala biyan bashi

Gwamnatin jihar ta sanya wa kanta burin kammala biyan dukkan haƙƙoƙin fansho da sauran kuɗaɗen da ake bin tsoffin ma’aikata kafin watan Afrilun 2027.

Sabon rabon Naira biliyan 5 na daga cikin matakan da gwamnatin ke ɗauka domin biyan kuɗaɗen ritaya da haƙƙoƙin iyalan ma’aikatan da suka rasu.

Shirin ya shafi tsofaffin ma’aikatan gwamnati da kuma iyalan ma’aikatan da suka rasu, waɗanda ke da haƙƙin karɓar kuɗaɗen da suka rage ba a biya su ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya shirya share hawayen 'yan Arewa, ya gano hanyar magance matsalar yankin

Abba ya samu goyon baya kan zaben 2027
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jawabi a wajen taro Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

An yi wa Gwamna Abba tayin mata

A wani labarin kuma, kun ji cewa fitaccen dan jarida kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, Reuben Abati, ya yi wa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf tayin mata.

Tsohon hadimin shugaban kasar ya yi barkwanci inda ya ba shi shawarar zai nemo masa sabuwar mata bayan samun matsala da daya tsohuwar matarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng