Martanin Gwamnatin Kaduna da ADC Ta Yi Zargin Ta Hana Wurin Taron Siyasa

Martanin Gwamnatin Kaduna da ADC Ta Yi Zargin Ta Hana Wurin Taron Siyasa

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta yi magana kan sahihancin wata wasika wacce ta nuna cewa ta hana ADC amfani da filin wasa na Ranchers Bees
  • Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu, Sadiq Mamman Lagos, ya ce wasikar karya ce kuma ba ta fito daga su ba
  • Gwamnatin ta bukaci jama’a da su yi watsi da takardar tare da guje wa yada labaran karya da ka iya haifar da rudani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta karyata wata wasika da ke yawo a kafofin sadarwa cewa an hana ADC taro a filin wasa.

Gwamnatin ta karyata cewa ta hana jam’iyyar ADC amfani da filin wasa na Ranchers Bees domin gudanar da gangaminta na ranakun 17 da 18 ga watan Nuwamba, 2026.

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu na jihar, Sadiq Mamman Lagos, ne ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Barazanar da ADC ta yi a Kaduna bayan hana ta taro a babban filin wasa

Mamman Lagos ya bayyana cewa an kirkiri wasikar ne domin yaudarar jama’a, yana mai jaddada cewa ba ta fito daga Ma’aikatar Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu ko ofishinsa ba.

A cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, kwamishinan ya ce:

“Ma’aikatar na son bayyana karara cewa wasikar da ake magana a kai KARYA CE, an kirkire ta ne, kuma ba ta fito daga ma’aikatar ko ofishin kwamishinan ba.”

Gwamnati ta gargadi jama’a

Kwamishinan ya ce ma’aikatar ta samu labarin yadda ake yada takardar, inda ya bukaci jama’a da su yi watsi da ita gaba daya.

Ya kuma gargadi mutane da su guji yada bayanan da ba su tantance sahihancinsu ba, yana mai cewa hakan na iya yaudarar jama’a tare da haddasa rudani a cikin al’umma.

A cewarsa, ya kamata jama’a su daina yada labaran karya da ake kirkira domin karkatar da tunanin mutane da haifar da rashin fahimta.

Wannan sanarwa ta gwamnatin Kaduna ta zo ne bayan rahotannin da suka bayyana cewa an hana ADC amfani da filin wasan na Ranchers Bees domin gudanar da gangamin siyasa a jihar.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.