Gwamnan Bauchi Ya Siffanta Tsohon Shugaban Najeriya Jonathan Da Shugaban Kirki

Gwamnan Bauchi Ya Siffanta Tsohon Shugaban Najeriya Jonathan Da Shugaban Kirki

  • Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed na jihar Bauchi ya sake bayyana amintarsa da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan
  • Jigon na PDP ya bayyana yabonsa ne ga Jonathan yayin da ya ziyarce shi a Bauchi domin masa ta'aziyyar rasuwan dan uwansa
  • Gwamnan na Bauchi ya ce babu shugaban da ya taba yin abin da Jonathan ya yi a lokacin da yake mulkar Najeriya

Jihar Bauchi - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya siffanta tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da shugaba mafi nagarta da Najeriya ta taba yi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da Jonathan ya ziyarce shi a Bauchi don yi masa ta'aziyyar rasuwar dan uwansa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Bala Mohammed na Bauchi ya yaba tsohon shugaban kasa Jonathan
Gwamnan Bauchi Ya Siffanta Tsohon Shugaban Najeriya Jonathan Da Shugaban Kirki | Hoto: Goodluck Jonathan
Asali: Facebook

A cewarsa:

"Kai ne dai abu mafi kyau da ya taba faruwa a kasar da ake kira Najeriya. Aikinka tukuru da sadaukarwarka ne suka sa Najeriya ta girma fiye da yadda ka same ta.

Kara karanta wannan

A Karon Farko, Wani Gwamnan Arewa Ya Bi Sahun Su Wike, Ya Nemi Shugaban PDP Na Kasa Ya Yi Murabus

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wasu da dama na fafutukar zama shugaban kasa a Najeriya amma babu wanda ya yi kusan irin halayenka.
"Kai fitacce ne, ka yi wa kasar nan aiki da iyakar karfinka wanda kuma da wahala a kwatanta ka da kowa."

Zuwan Jonathan Bauchi

Tsohon shugaban kasan ya dura filin jirgin Sir Abubakar Tafawa Balewa a jihar Bauchi ne da misalin karfe 9:45 na safe, kuma mataimakin gwamnan jihar, Sanata Baba Tela da sauran kusoshin gidan gwamnati ne suka tarbe shi.

Jonathan, ya taho ne tare da shugaban hukumar jin dadin alhazai ta kirista, Rabaran Kennedy Opara da Bawa Bwari, tsohon dan majalisar wakilai.

Gwamna Bala ya tarbi Jonathan a gidan gwamnati na Ramat dake a jihar ta Bauchi.

Daga baya, an ga lokacin da Jonathan ya yada hotunan ziyarar tasa ta jihar Bauchi a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: "Ni Ba Waliyyi Bane, Ina Da Nakasu Da Dama", Ayu Ya Yi Martani Kan Zargin Rashawa Da Wike Ya Masa

Kalli hotunan:

Atiku, Ayu, Okowa da Gwamnonin PDP Sun Taru a Bauchi, Za Su Tattauna

A wani labarin, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya gana da gwamnonin PDP a Arewa maso Gabas da sauran jiga-jigan siyasar yankin.

Wannan ganawa na zuwa daidai lokacin da Atiku ke ci gaba da samun ciwon kai daga gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike kan wasu bukatun da ya gabatar ciki har da na sauke shugaban PDP na kasa.

Wadanda suka halarci ganawar da aka yi a yau Laraba 5 ga watan Oktoba sun hada da:

Asali: Legit.ng

Online view pixel