'Yan Bindiga Sun Sake Barna a Zamfara bayan Kashe Hadimin Gwamna Dauda

'Yan Bindiga Sun Sake Barna a Zamfara bayan Kashe Hadimin Gwamna Dauda

  • ’Yan bindiga sun kashe wani jami’in tsaro tare da kai hari gidan ɗan kasuwa Alhaji Babangida Sama’ila a Sabuwar Kaura
  • Maharan sun yi awon gaba da mata da yara, ciki har da wasu ’yan mata masu shekaru 14 zuwa 16, amma daga baya aka saki mahaifiyarsu
  • Harin ya zo ne kwana guda bayan kashe babban hadimin Gwamna Dauda Lawal da wasu masu ibada shida a wani masallaci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Zamfara - Wasu ’yan bindiga sun kashe wani jami’in tsaro tare da sace wasu ’yan gidan wani ɗan kasuwa, Alhaji Babangida Sama’ila, a Sabuwar Kaura, ƙaramar hukumar Kaura Namoda ta Jihar Zamfara.

Maharan sun kai farmakin ne ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamban 2026 a gidan ɗan kasuwar, inda suka yi awon gaba da wasu ’yan mata uku, mahaifiyarsu da yara maza biyu, tare da wani baƙo da ya ziyarci iyalin.

Kara karanta wannan

"Ku kasance cikin shiri": Abin da Kwankwaso ya gayawa magoya baya bayan kai masa hari

'Yan bindiga sun sace mutane a Zamfara
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Sai dai daga baya aka samu labarin cewa maharan sun saki mahaifiyar yaran, jaridar Leadership ta kawo rahoton.

Yadda maharan suka kai farmaki

Wani mazaunin Sabuwar Kaura ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa harin ya ɗauki kusan awa ɗaya.

Ya ce jami’in tsaron da ke gadin gidan ya rasa ransa ne lokacin da ya yi ƙoƙarin hana maharan shiga gidan.

A cewarsa, bayan sun kasa shiga ta ƙofar gidan, maharan sun yi amfani da wani gini na wucin gadi wajen tsallaka katangar gidan.

Ya ƙara da cewa Alhaji Sama’ila da ɗaya daga cikin ’ya’yansa sun tsira ne ta hanyar tsallakawa katangar gidan.

Mazaunin ya bayyana cewa uku daga cikin ’yan matan da aka sace ba su kai shekara 18 ba. Ya ce shekarunsu na tsakanin 14 zuwa 16, haka ma baƙon da aka yi awon gaba da shi yana da kusan shekaru 15 zuwa 16.

Damuwa kan jinkirin kai ɗauki

Kara karanta wannan

Sama da mutum 50 sun mutu da yan sa kai suka yi arangama da wasu yan bindiga

Mazaunin ya nuna damuwa kan yadda maharan suka shafe kusan awa ɗaya suna gudanar da farmakin ba tare da jami’an tsaro sun kai ɗauki cikin gaggawa ba.

Ya ce gidan yana kusa da Babban Asibitin Kaura Namoda, amma duk da haka maharan sun samu damar gudanar da harin na tsawon lokaci.

Ya yi zargin cewa harbin gargadi da sojojin da ke gadin gidan shugaban Kwalejin Fasaha ta Tarayya da ke Kaura Namoda suka yi, tare da taimakon ’yan sa-kai, na iya zama abin da ya kawo cikas ga maharan.

Zargin hanyoyin shigowar ’yan bindiga

Mazaunin ya ambaci wasu ƙauyuka da unguwanni da ke kewaye da garin, ciki har da Gidan Sambo, Unguwar Sarkin Musulmi da Madira, a matsayin wuraren da ake zargin ’yan bindigar ke bi wajen shiga garin.

Ya kuma yi zargin cewa wasu al’ummomi da ke kewaye da Kaura Namoda sun shiga yarjejeniyoyin sulhu da ’yan bindiga.

A cewarsa, irin waɗannan yarjejeniyoyi na iya haifar da barazana ga tsaron yankin idan ba a kula da su yadda ya kamata ba.

Ya ce Unguwar Sarkin Musulmi tana da nisan ƙasa da kilomita ɗaya daga sansanin wani fitaccen shugaban ’yan bindiga da aka bayyana da suna Dan Sadiya.

Kara karanta wannan

Mutanen Kano na cikin alheri, Gwamna Abba ya shirya rabon tallafin N50,000

Wani mazaunin garin kuma ya nuna zargin cewa wasu ’yan bindiga na iya zama a ɓoye a cikin garin, lamarin da ke wahalar da jami’an tsaro wajen gano motsinsu.

Harin ya biyo bayan kisan hadimin gwamna

Wannan farmaki ya faru ne kwana guda bayan wasu ’yan bindiga sun kashe Nasiru Sani Kaura, babban hadimin Gwamna Dauda Lawal, tare da wasu masu ibada shida a wani masallaci da ke garin.

Kisan hadimin gwamnan ya jawo fushin jama’a, inda wasu mazauna yankin suka yi wa gwamnan ihu yayin sallar jana’izar mamacin ranar Lahadi.

'Yan bindiga sun yi barna a Zamfara
Taswirar jihar Zamfara, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An cafke matar da sace yar dan'uwanta

A wani labarin kuma, kun ji cewa rundunar ’yan sandan jihar Zamfara ta kama wata mata mai shekara 26 bisa zargin sace ƙaramar ’yar yayanta mai shekara uku, tare da neman kuɗin fansa har Naira miliyan 10.

An ce yarinyar ta shafe kusan makonni biyu a hannun wadda ake zargi kafin jami’an ’yan sanda su yi nasarar kuɓutar da ita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng