Shugaba Tinubu Ya Kara Yawan Jihohin da Zai Je Yakin Neman Zabe gabanin 2027

Shugaba Tinubu Ya Kara Yawan Jihohin da Zai Je Yakin Neman Zabe gabanin 2027

  • Shugaba Bola Tinubu ya ƙara yawan jihohin da zai ziyarta domin yaƙin neman zaɓensa na 2027 daga 12 zuwa 19
  • Sabon jadawalin ya tanadi cewa shugaban zai halarci tarukan yaƙin neman zaɓe guda 20 a faɗin Najeriya tsakanin 24 ga Oktoba, 2026 da 13 ga Janairu, 2027
  • Jihohin Katsina, Taraba, Zamfara, Imo da Kwara na cikin sababbin wuraren da aka ƙara a jerin jihohi 12 da aka fitar tun farko

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Tinubu ya faɗaɗa jadawalin ziyarar da zai kai jihohin Najeriya domin yaƙin neman zaɓensa na shugaban ƙasa a 2027.

An ƙara yawan jihohin da shugaban ke shirin ziyarta daga 12 zuwa 19, ban da Babban Birnin Tarayya (FCT), Abuja.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin gangamin yakin neman zaben APC a jihar Kebbi Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaiato cewa sabon jadawalin ya nuna cewa shugaba Tinubu zai ƙara halartar tarukan yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC a faɗin ƙasar.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: ADC ta bayyana matsayarta kan takarar Atiku duk da hukuncin kotu

Yanzu ana sa ran shugaban zai halarci gamgamin yaƙin neman zaɓe guda 20 a sassan Najeriya. Jadawalin da aka sabunta ya ƙunshi lokaci daga ranar 24 ga Oktoba, 2026 zuwa 13 ga Janairu, 2027.

Daga cikin manyan jihohin da aka ƙara akwai Katsina, Taraba, Zamfara, Imo da Kwara. Haka kuma, an shigar da Akwa Ibom, Jigawa da Kebbi cikin jadawalin bayan da Tinubu ya halarci gamgamin yaƙin neman zaɓe a jihohin a baya-bayan nan.

Wannan sabon tsari ya sauya tsarin farko da aka tsara cewa wasu shugabannin APC za su wakilci Tinubu a gamgamin kamfe a wasu jihohi.

A ranar 6 ga Nuwamba, Tinubu ya halarci taron yaƙin neman zaɓen jam'iyyar a Uyo, jihar Akwa Ibom, inda kuma ya ƙaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Gwamna Umo Eno ta gudanar.

A ranar 7 ga Nuwamba, jirginsa ya dura Fatakwal, jihar Rivers. Daga nan ya wuce Dutse, jihar Jigawa, a ranar 10 ga Nuwamba, da kuma Birnin Kebbi, jihar Kebbi, a ranar 17 ga Nuwamba.

Kara karanta wannan

"Akwai damuwa game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya gabanin zaben 2027"

Sabon jadawalin jihohin da Tinubu zai je

Sabon jadawalin ya tanadi cewa shugaban zai je kamfe a Katsina a ranar 2 ga Disamba, Kano a ranar 17 ga Disamba, Jalingo a ranar 19 ga Disamba, sannan Abuja a ranar 21 ga Disamba.

Sauran wuraren da aka tsara zai ziyarta sun haɗa da Gusau, jihar Zamfara, a ranar 28 ga Disamba, da Owerri, jihar Imo, a ranar 30 ga Disamba.

Ana sa ran Tinubu zai ci gaba da yaƙin neman zaɓensa a sabuwar shekara, inda zai je Yola, jihar Adamawa, a ranar 4 ga Janairu; Sokoto a ranar 5 ga Janairu; da Ilorin, jihar Kwara, a ranar 8 ga Janairu.

Daga nan shugaban zai ziyarci Asaba, jihar Delta, a ranar 11 ga Janairu, kafin ya kammala yaƙin neman zaɓensa da babban taro a Legas a ranar 13 ga Janairu, 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262